Sulhu Ya Yi Rana: 'Yan Bindiga Sun Sako Mutanen da Suka Sace a Katsina

Sulhu Ya Yi Rana: 'Yan Bindiga Sun Sako Mutanen da Suka Sace a Katsina

  • Ana ci gaba da kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin al'ummomi da 'yan bindiga masu dauke da makamai a wasu sassan jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Daya daga cikin jagororin 'yan bindiga a jihar Katsina, Alhaji Isiya Kwashen Gwarwa, ya sako wasu mutanen da ke hannunsa domin mutunta yarjejeniyar sulhu
  • Sako mutanen dai wadanda suka hada da maza, mata da yara ya biyo bayan yarjejeniyar sulhu da aka kulla da 'yan bindiga a yankin a kwanakin baya

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun sako akalla mutane 45 da suka haɗa da maza, mata da yara a jihar Katsina

An mika mutanen da 'yan bindigan suka sako ga hukumomi a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

'Yan bindiga sun sako mutane a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa an sako mutanen ne ta hannun daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga, Alhaji Isiya Kwashen Garwa, a wani kauye da ke kan iyaka tsakanin Faskari da Bakori.

Kara karanta wannan

Annobar garkuwa da mutane ta sake kunno kai, an kwashe kusan mutum 150 a 'yan kwanaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sako mutane a Katsina

An shaida mika mutanen ne a ranar Litinin ta hannun dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Bakori, Injiniya Abdurrahman Kandarawa.

Zagazola Makama ya rahoto cewa sakin mutanen ya biyo bayan cika alkawarin da tubabbun ’yan bindigan suka yi yayin wani zaman tattaunawar sulhu don samun zaman lafiya a baya.

Da yake jawabi bayan karɓar mutanen, Abdulrahman Kandarawa ya gode wa tubabbun ’yan bindigan kan mutunta yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da gwamnati.

Ya tabbatar musu da cewa karamar hukumar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya na dindindin.

Haka kuma ya jaddada muhimmancin tattaunawa da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Hausawa da Fulani, inda ya tunatar da dogon tarihin zumunci da alakar da ke tsakaninsu.

Jagoran 'yan bindiga ya yi jawabi

A nasa bangaren, Isiya Kwashen Garwa ya yi kira ga duk matakan gwamnati su tabbatar da tsaro da kuma ba wa sauran tubabbun abokan aikinsa damar shiga garuruwa ba tare da tangarɗa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban sojoji ya dura Kebbi, ya ba dakaru umarni kan daliban da aka sace

Ya ce hakan zai karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a tsakanin dukkan ɓangarorin.

'Yan bindiga sun cika yarjejeniyar sulhu a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun yanka mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Katsina bayan sun hallaka wasu shugabannin al'umma.

Harin ya harin ya auku ne a kauyen Doguwar Ɗorawa, kusa da Guga a ƙaramar hukumar Bakori, inda aka kashe dattawa biyu masu fada-a ji a kauyen, Alhaji Bishir da ɗan uwansa, Alhaji Surajo.

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, kuma sun ci karensu babu babbaka har tsawon awa ɗaya, ba tare da an kai dauki ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng