An ‘Gano’ Jihohi 8 da ’Yan Ta’adda Za Su Iya Kai Mummunan Hari a Najeriya

An ‘Gano’ Jihohi 8 da ’Yan Ta’adda Za Su Iya Kai Mummunan Hari a Najeriya

  • Wani malamin addinin Kirista ya sake hasashe kan wasu jihohin da za su fuskanci hare-haren yan ta'addan idan ba a dauki mataki ba
  • Fasto Elijah Ayodele ya gargadi hukumomin tsaro su maida hankali kan jihohin Najeriya takwas saboda barazanar hare-haren ’yan ta’adda
  • Malamin addinin ya tabbatar da cewa hakan ka iya haddasa mummunar tarzoma a ƙasar domin harin zai jawo matsaloli da yawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya gargadi jami’an tsaro su kula sosai kan hasashen harin yan ta'adda.

Malamin ya ce dole a kula da wasu jihohi saboda barazanar hare-haren ’yan ta’adda da ka iya faruwa wanda zai jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Fasto ya jero jihohi 8 da yan ta'adda za su kai hari
Fitaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Twitter

Fasto ya yi hasashen kawo hari a jihohi

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai Osho Oluwatosin ya fitar wanda Tribune ta samu inda ya gargadi hukumomi.

Kara karanta wannan

Kisan Kiristoci: CAN ta kira Trump kan taimakon Najeriya, yaki da ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya ce mutanen banza na shirin kai manyan hare-hare, kuma gazawar sojoji na iya haifar da babbar matsala.

Ya lissafa jihohin Nasarawa, Abuja, Ondo, Kaduna, Sokoto, Benue, Katsina da Yobe, yana cewa wajibi ne a ƙara tura ƙarin dakarun soja domin shawo kan barazanar.

Ayodele ya ce za a yi amfani da matsalar tsaro wajen takura gwamnatin Tinubu, inda ya yi gargadin cewa ƙarin hare-hare kan sojoji zai faru idan ba a dauki mataki ba.

A cikin sanarwar, Ayodele ya ce:

"Wadannan jihohi sun hada da Nasarawa, Abuja, Ondo, Kaduna, Sokoto, Benue, Katsina da kuma jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.
"Ya kamata wadannan jihohi takwas a ba su kulawa ta musamman, ya kamata a tura karin jami'an tsaro a cikinsu."
Fasto ya yi gargadi kan harin Amurka a Najeriya
Fasto Elijah Ayodele yayin da yake wa'azi. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Amurka: Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu

Faston ya kuma bayyana cewa zuwan Amurka domin taimakawa Najeriya zai kasance abin kunya, yana mai jaddada cewa tuni ya yi hasashen yiwuwar kashe manyan hafsoshin sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya karyata dan majalisar Amurka kan sace daliban Kebbi a 'yankin Kiristoci'

Ayodele ya yi ikirarin cewa idan sojojin Najeriya suka kasa yin abin da ya dace, Amurka za ta shiga lamarin, kuma hakan zai raunana karfin rundunar tsaro da gwamnatin Tinubu.

"Za su yi amfani da rashin tsaro domin yakar wannan gwamnati, ya kamata ya dauki maganar rashin tsaro da muhimmanci, za a samu farmaki kan sojojin Najeriya."

Ya ce zuwan Amurka zai kara raunana karfin sojojin Najeriya inda ya shawarci hukumomi su tsaya tsayin daka kan lamarin, cewar Daily Post.

Fasto ya samu wahayi kan zaben 2027

A baya, kun ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya yi magana kan waɗanda za su tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ke tafe wanda zai yi zafi matuka.

Ayodele ya ce takarar shugaban kasa ta 2027 za ta kasance tsakanin Bola Tinubu da wasu mutane biyu da aka nuna masa domin ganin sun dare kan karagar mulki a Najeriya.

Ya gargadi tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ka da ya tsaya takara, domin yin hakan zai sauƙaƙa wa Tinubu samun wa'adi na biyu a zaben shugaban kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.