Sauki Ya Samu: Shinkafa da Sauran Kayan Abinci Sun Kara Araha a Kwara da Wasu Jihohi 2

Sauki Ya Samu: Shinkafa da Sauran Kayan Abinci Sun Kara Araha a Kwara da Wasu Jihohi 2

  • Jama'a sun fara murna da farin ciki sakamakon raguwar farashin kayan abinci a kasuwanni a jihohin Kwara, Ogun da Oyo
  • Masu ruwa da tsaki kan harkar noma sun danganta arahar da aka samu da amfanin gona da shigo da kaya daga waje
  • Bincike ya nuna cewa farashin shinkafa, gari da kayan lambu kamar tumatir da albasa sun sauka a wadannan jihohi uku

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Masu ruwa da tsaki a bangaren abinci da noma a jihohin Ogun, Oyo da Kwara sun yi farin ciki sa yadda farashin kayan abinci ya ragu.

Sun kuma yabawa Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu bisa manufofinta da matakan da ta dauka, wanda ya taimaka wajen kawo arahar kayan abinci.

Kayan abinci.
Hoton wasu kayayyakin abinci da yan kasuwa ke sayarwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

The Nation ta ce a binciken da aka gudanar a ranar Talata a kasuwannin Lafenwa, Kuto da Olomore a Abeokuta, jihar Ogun, farashin shinkafa, wake, garri, man gyada da dankali sun rage tsada.

Kara karanta wannan

Annobar garkuwa da mutane ta sake kunno kai, an kwashe kusan mutum 150 a 'yan kwanaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma an ga saukar farashin kayan ganye da suka hada da tattasai, albasa da tumatir.

Kayan abinci sun yi araha a Ogun

Binciken ya nuna cewa ma'aunin da ake kira 'kongo' na garri ya dawo N500, daga N1,800 a watan Agusta, yayin da buhun garri ya koma N28,000 daga N40,000.

Buhun shinkafa 50kg ya ragu zuwa N53,000 daga N68,000, yayin da wake Oloyin ya koma N60,000 daga N70,000. Man gyada lita biyar ya koma N13,000 daga N16,000, yayin da man jarka ya sauka daga N70,000 zuwa N66,000.

Babban kwandon albasa ya koma N12,000 daga N20,000, yayin da kananan kwanduna suka sauka daga N10,000 zuwa N5,000. Bahin atarugu ya dawo tsakanin N35,000 – N40,000, daga N60,000 – N65,000.

Sakataren kungiyar manoma ta AFAN na Ogun, Abiodun Ogunjimi, ya danganta raguwar farashin da zuwan lokacin girbi, saukar kudin sufuri da shigo da kaya daga waje.

Ya yi gargadi cewa ba tare da tsare-tsaren gwamnati ba, wannan saukin da aka samu na iya zama na wucin-gadi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

An samu sauki a Kwara da Oyo

A Ilorin, shugabar 'yan kasuwa a Jihar Kwara, Alhaja Muhibat Olumon, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakan da suka kai ga saukar farashin kayan abinci.

Ta bayyana cewa, a matsayinta na shugabar ‘yan kasuwa a jihar, suna gudanar da tarurruka akai-akai da dillalai a fadin Kwara domin hana su tada farashin kaya ba gaira ba dalili

“Dole mu tsabtace kasuwanni da daga ‘yan kasuwa masu son zuciya ta hanyar dagula farashi, sannan su dora laifi a kan gwamnati.”

A jihar Kwara, buhun shinkafa ya sauka daga N70,000 a Oktoba zuwa N54,000. Sabon garin Elubo ya sauka daga N140,000 zuwa N120,000, yayin da tsohon Elubo ya tsaya a N160,000.

Kayan abinci.
Hoton doya, dankalin turawa, albasa da tumatiri a kasuwa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farfesa Alarudeen Aminu, malami a Sashen Tattalin Arziki na Jami’ar Ibadan, jihar Oyo ya ce raguwar farashin kayan abinci ya samo asali ne daga lokacin da aka shiga na girbi.

"Idan kayayyaki sun yi yawa fiye da bukata, farashi yana sauka domin a samu masu saye. Wannan shi ne muke gani yanzu,” in ji Farfesa Aminu.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun karya farashi, ana sayar da kayan abinci da araha a jihar Benue

Hauhawar farashi ya ragu a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kididdiga ta kasa watau NBS ta fitar da alkaluman hauhawan farashin kayayyaki a Najeriya na watan Oktoba da ya gabata.

Rahoton NBS ya nuna cewa farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da faduwa kasa warwas a kasuwannin Najeriya.

NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sauka zuwa kashi 16.05 a watan Oktoba 2025 daga kashi 18.02 da aka samu a Satumba, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262