Gwamnonin Arewa Sun Fitar da Matsaya kan Daliban Kebbi da aka Sace

Gwamnonin Arewa Sun Fitar da Matsaya kan Daliban Kebbi da aka Sace

  • Gwamnonin Arewa sun magantu kan harin da aka kai GGCSS Maga a Danko/Wasagu, inda aka sace dalibai kuma aka kashe jami’i
  • Shugaban kungiyar gwamnonin ta NSGF, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce wannan danyen aikin barazana ne ga makomar ilimi a yankin
  • Gwamnonin sun jajanta wa Gwamna Nasir Idris na Kebbi da iyalan wadanda abin ya shafa, tare da neman ceto daliban cikin gaggawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnonin Arewa sun bayyana takaici mai tsanani kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai a makarantar GGCSS da ke Maga a Danko/Wasagu, jihar Kebbi.

Harin da aka kai da asuba ya yi sanadin sace dalibai mata da kuma kashe mataimakin shugaban makarantar.

Gwamnonin Gombe da jihar Kebbi
Shugaban gwamnonin Arewa da gwamnan jihar Kebbi. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban gwamnonin Arewa, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya daukarwa iyayen yaran da aka sace alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, rashin hankali, kuma abin da ba za a taba amincewa da shi ba.

Ya ce kai hare-hare ga makarantu yana kara barazanar rushe ci gaban ilimi da ake kokarin ginawa a yankin.

Daliban Kebbi: Matsayar gwamnonin Arewa

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi nuni da cewa wajibi ne makarantu su kasance wajen samun ilimi, ba wuraren tashin hankali ba.

Ya yi gargadi da cewa irin wadannan hare-haren na iya dagula kokarin da yankin ke yi na bunkasa shigar yara makaranta da rage yawan wadanda ba sa zuwa makaranta.

Tribune ta wallafa cewa ya kara da bayyana damuwarsa kan halin wahala da tsoron da daliban da aka sace za su iya fuskanta.

A cewarsa, wannan lamari ya sake jaddada bukatar karfafa tsaro a cibiyoyin ilimi domin kare rayuka da makomar 'ya'yan Arewa.

Kira kan daukar matakin gaggawa

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka mamaye GGCSS Maga da harbi kafin sace dalibai mata a Kebbi

Shugaban NSGF ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da aiki cikin gaggawa, tare da tsari mai kyau, domin ceto daliban cikin koshin lafiya da kuma cafke wadanda suka aikata laifin.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a dauki tsauraran matakan kawo karshen ta'addanci da ke barazana ga rayuka da ilimi.

Motar makarantar da aka sace dalibai
Motar makarantar mata ta Maga da aka sace dalibai. Hoto: Amnesty International|Zagazola Makama
Source: Facebook

A cewarsa, hadin kai tsakanin jihohin Arewa, gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro zai ci gaba da kasancewa babban ginshikin kare jama’a, musamman yara mata da suke neman ilimi a yankin.

Gwamnoni sun yi kira ga 'yan Arewa

Gwamnan ya roki Allah SWT ya taimaka a ceto daliban cikin hanzari, yana mai mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka jikkata ko suka rasa ’yan uwa a harin.

Ya kuma bukaci al’umma a dukkan sassan Arewa da su kasance masu sa ido tare da bayar da bayanai ga hukumomin tsaro idan sun ga duk wani abin da ake zargi.

Shugaban sojoji ya ziyarci jihar Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa shugaban rundunar sojojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya ziyarci jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kausasa harshe kan sace dalibai mata a Kebbi, ya gwamnatin Tinubu shawara

Ya kai ziyayar ne bayan bayyanar labarin sace daliban jihar da ke karatu a wata makarantar mata a ranar Litinin.

Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya ce dakarun sojojin Najeriya za su yi dukkan kokarinsu wajen ceto daliban da aka sace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng