Matawalle Ya Isar da Sakon Tinubu ga Dakarun Sojoji a Zamfara

Matawalle Ya Isar da Sakon Tinubu ga Dakarun Sojoji a Zamfara

  • Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya ziyarci hedkwatar rundunar Operation Fansan Yamma mai aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma
  • Bello Matawalle ya sanar da dakarun sojojin sakon da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi
  • Karamin ministan tsaron ya bayyana cewa jarumtar dakarun sojojin rundunar ta sanya an tarwatsa sansanoni da dama na manyan jagororin 'yan bindiga

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Karamin ministan tsaro, kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sanarwa dakarun sojoji sakon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa gare su.

Bello Matawalle ya bayyana cewa Mai girma Bola Tinubu ya yaba da jarumtakar dakarun Operation Fansan Yamma wajen tarwatsa sansanonin ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Matawalle ya gana da dakarun sojoji a Zamfara
Bello Matawalle na yi wa dakarun sojoji jawabi Hoto: Ahmad Dan Wudil
Source: UGC

Jaridar TheCable ta ce karamin ministan tsaron ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a hedkwatar rundunar Operation Fansan Yamma mai aikin samar da tsaro a Arewa maso Yamma da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Shugaban sojoji ya dura Kebbi, ya ba dakaru umarni kan daliban da aka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Bello Matawalle ya gayawa sojoji?

Matawalle ya ce sadaukarwar sojoji ce ta sanya zaman lafiya ya fara dawowa a jihar da ma makwabtanta.

"Musamman shugaban kasa ya umarce ni da na sanar muku cewa kun yi abin a yaba sosai."
“An hallaka yawancin manyan jagororin ’yan bindiga da mayakansu ta hanyar jarumtar ku.”

- Bello Matawalle

Jaridar The Punch ta ce Matawalle ya ce abin da ya rage yanzu kawai wasu kananan ragowar ’yan bindiga ne, kuma shugaban kasa ya ba da umarnin a kawar da su baki ɗaya.

“Shugaban kasa ya tabbatar muku da cikakken tallafi, kayan aiki, sufuri, jin daɗi da duk abin da ke kara kwarin gwiwa domin kammala aikin.”

- Bello Matawalle

Matawalle ya yi jawabi ga dakarun sojoji
Bello Matawalle tare da dakarun Operation Fansan Yamma Hoto: Ahmad Dan-Wudil
Source: Facebook

Bello Matawalle ya jaddada kudirin gwamnati

Ministan ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da samar da kayayyaki, karin walwala, sababbin kayan yaki da abubuwan tattara bayanan sirri na zamani domin kara kuzarin yaki da ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kara gwangwaje Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da mukami

Yayin da yake magana da jami’ai da sojoji a filin fareti, Matawalle ya bukace su da su kasance masu tsayawa tsayin daka, taka-tsantsan, da kuma bin doka, yana mai jaddada cewa cikakkiyar nasara kan ’yan bindiga tana dab da tabbata.

Karanta wasu labaran kan Matawalle

Minista ya yi martani kan satar dalibai a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya nuna takaicinsa kan sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.

Bello Matawalle ya yi Allah wadai da ta'addancin 'yan bindigan wanda ya ritsa har da mataimakin shugaban makarantar sakandiren mata da ke Maga, a karamar hukumar Danku/Wasagu.

Karamin ministan tsaron ya bada tabbacin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta ceto daliban ba tare da bata lokaci ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng