Yadda 'Yan Bindiga Suka Mamaye GGCSS Maga da Harbi kafin Sace Dalibai Mata a Kebbi
- A ranar Litinin ’yan bindiga suka shiga makarantar GGCSS Maga a jihar Kebbi, suka tafi da dalibai mata kimanin 25
- Wasu mutanen da suke yankin da abin ya faru sun bayar da labarin 'yadda 'yan ta'addan suka isa makarantar sakandaren
- An ce an kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makuku, lokacin da yake ƙoƙarin kare ɗalibansa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – A safiyar jiya ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar GGCSS Maga, da ke yankin Danko/Wasagu, inda suka yi awon gaba da dalibai mata 25.
Harin ya auku ne a daidai lokacin da maharan suka kutsa cikin makarantar ba tare da wata turjiya ba.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa wani abin takaici shi ne kisan mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin kare ɗaliban yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidu sun bayyana cewa harbin da aka yi ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tsananin damuwa.
Yadda aka kai hari makarantar Kebbi
Wani mazaunin yankin, Aliyu Yakubu, ya ce maharan sun kutsa cikin makarantar ne misalin ƙarfe 5:00 na asuba.
Ya tabbatar da cewa Malam Makuku ya sha ruwan harsashi ne a lokacin da yake ƙoƙarin hana su kwashe ɗalibai.
Ya ce:
“An harbe shi ne a lokacin da yake ƙoƙarin kare ɗaliban daga maharan. Wannan babban rashi ne a gare mu da makarantar.”
Wani shaidan gani da ido, Sulaiman Abdullahi, ya ce maharan sun zo da yawan gaske inda suka fara harbe-harbe kafin su kutsa makarantar.
Ya ce:
“Sun zo da daren jiya suna harbi a ko ina kafin su sami damar shiga makarantar. An ga gawarwaki da dama, amma ba a tabbatar da yawansu ba tukuna.”
Ya ƙara da cewa jiragen saman sojojin sama sun bayyana a sararin sama misalin ƙarfe 8:00 na safe bayan harin, yayin da jami’an tsaro suka kewaye yankin gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta daukarwa 'yan Najeriya alkawari kan sace dalibai mata a Kebbi

Source: Facebook
Martanin hukumomi da al’ummar Kebbi
Mazauna yankin sun taru suna addu'ar neman rahama ga Malam Makuku, suna roƙon Allah ya jikansa tare da bai wa iyalansa hakuri da juriya.
Punch ta rahoto cewa kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa maharan sun tsallake katanga sannan suka fara harbi kafin su yi garkuwa da dalibai 25.
Ya ce:
“An tura rundunar musamman ta yi artabu da su, amma kafin wannan lokaci maharan sun riga sun fice da daliban zuwa cikin daji.”
Iyaye da mazauna yankin yanzu haka suna jiran cikakken bayani daga hukumomi kan yadda ake ci gaba da neman waɗanda aka sace.
Umarnin Tinubu kan daliban Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomin tsaro umarni kai tsaye da su ceto daliban GGCSS Maga.

Kara karanta wannan
Atiku ya kausasa harshe kan sace dalibai mata a Kebbi, ya gwamnatin Tinubu shawara
A cewar Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris shugaban ya yi Allah wadai da abin da ya faru da daliban yayin da suke karatu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nanata cewa kare rayuwar ’yan ƙasa musamman ɗalibai, muhimmin hakkin gwamnati ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
