Annobar Garkuwa da Mutane Ta Sake Kunno Kai, An Kwashe kusan Mutum 150 a 'Yan Kwanaki
- Najeriya na sake fuskantar yawaitar garkuwa da mutane, bayan an fara samun saukin kwashe mutane masu tarin yawa da 'yan ta'adda ke yi
- Miyagun 'yan bindiga sun kwashe mutane fiye da 145, an yi awon gaba da su daga jihohin Kebbi, Neja da Zamfara cikin kwanaki huɗu
- Sabon tashe-tashen hankula na zama babbar barazana yayin da ake shirin shiga zaben 2027, bayan irin yawan sace-sacen da aka gani a 2023
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Najeriya na sake shiga yanayin tashin hankalin da ya yi kama da wanda aka gani kafin zaben 2023, inda garkuwa da mutane ya yi ƙamari.
A cikin kwanaki huɗu kacal, an sace mutane akalla 145 a jihohin Kebbi, Neja da Zamfara, abin da ya tayar da hankula game da tsaro da tasirin siyasa yayin da ake shirin babban zabe.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa a Kebbi, maharan sun kai hari da sassafe a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga, ƙaramar hukumar Danko/Wasagu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ta'adda sun dawo da garkuwa da mutane
A yayin harin da aka kai Kebbi, 'yan ta'adda sun sace ɗalibai mata 25 tare da kashe wani ma’aikacin makaranta, yayin da jami'in tsaron makarantar ya samu rauni.
Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa rundunonin ta sun yi musayar wuta da maharan amma suka tsere da ɗaliban.
An ce ƙarin jami’ai, sojoji da ‘yan sa-kai sun shiga dazuzzukan da ake zargin maboyar ’yan bindiga domin ceto waɗanda aka sace.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Bello Sani, ya tabbatar da an ɗauki matakan da suka dace, tare da kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu.

Source: Facebook
A jihar Neja kuwa, kwana biyu kafin harin Kebbi, akalla ’yan sa-kai 16 aka kashe sannan aka yi garkuwa da mutum 42 a Mashegu.
A Zamfara kuma, an kashe mutane uku a Fegin Baza sannan aka yi garkuwa da mutum 64, yayin da a wani sabon hari a Tsohuwar Tasha, Maru, aka sace mutane 14, ciki har da mata 11 da yara uku.
Rahotanni sun nuna cewa al’umman Zurmi, Shinkafi, Maradun, Tsafe da Bungudu sun shafe watanni suna fama da hare-hare da tilasta biyan kudin fansa.
Gwamnati ta yi magana kan rashin tsaro
Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa matuƙa kan sace ɗaliban mata a Kebbi, inda Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya dage kan kare rayukan jama'a.
Ya ce an bai wa jami’an tsaro umarni na musamman su nemo su ceto ɗaliban tare da gurfanar da maharan a gaban hukuma.
Mohammed Idris ya kara da cewa gwamnati na ƙara ƙaimi wajen inganta kayan aikin tsaro da haɗin gwiwa da ƙasashen ECOWAS, AU da MNJTF domin kakkabe ’yan ta’adda.
Yahaya Sarki, Mashawarcin gwamnan Kebbi a kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki ya shaida wa Legit cewa gwamnati ba ta dauki sace daliban da sauki ba.
A kalamansa:
"Lokacin da wannan abu ya faru, 'yan bindiga sun shiga makarantar suka bude wuta, suka kashe mutum daya da ke aiki a makarantar. Gaskiya faruwar wannan abu, mai girma gwamna yana Abuja, ya katse aikinsa, ya zo tare da jami'an tsaro. Da farko ya fara turo mataimakinsa, sannan daga baya ya biyo tare da mukarraban gwamnati.'
"Ya fara zama tare da iyayen yara da masu ruwa da tsaki a wannan yanki, ya ba su tabbaacin irin yunkurin da gwamnati ke yi domin a kubutar da yara ba.
An sace dalibai a Kebbi
A baya, mun wallafa cewa wasu 'yan bindiga dauke a miyagun makamai sun kutsa wata makaranta a jihar Kebbi, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mai girma Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana harin a matsayin abin takaici kuma rashin imani tare da jajanta wa iyayen da aka sace yaransu.
Ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya, yayin da ta bayyana matakan da ta dauka don ganin an ceto daliban cikin koshin lafiya daga hannun yan ta'addan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


