Shugaban Sojoji Ya Dura Kebbi, Ya ba Dakaru Umarni kan Daliban da aka Sace
- Babban hafsan sojojin kasan Najeriya ya isa Jihar Kebbi domin duba aikin ceto daliban GGCSS Maga da aka sace
- Shugaban sojojin ya umarci dakarun kasar su kasance bakin aiki da farautar 'yan ta'adda domin ceto 'yan yaran
- Ya jaddada muhimmancin hadin kai da ‘yan sa-kai wajen kawo karshen barazanar 'yan ta'adda masu garkuwa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Hafsan sojojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ziyarci Jihar Kebbi a ranar Litinin domin karfafa aikin ceto daliban makarantar GGCSS Maga da aka sace.
Wannan ziyarar ta zo ne yayin da jami’an Operation FANSAN YANMA ke ci gaba da kai samame a dazuka domin kubutar da yaran.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Laftanar Janar Shaibu ya isa jihar tare da tawagar manyan jami’an hedkwatar soji.

Kara karanta wannan
Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a dauki matakai masu tsauri don tilastawa miyagun da suka aikata laifin sakin daliban.
Jawabin shugaban sojoji a Kebbi
Yayin jawabin sa ga sojoji, COAS ya yi bayani cikin karfin gwiwa da nuna takaici, yana mai cewa wajibi ne aikin ceto daliban ya yi nasara.
“Sai kun yi yaki da rana da dare. Dole mu nemo wadannan yara,”
- Inji shi.
Ya nanata cewa sojoji ba su da wani zabi face gudanar da aiki cikin tsantsar jajircewa da nufin nasara.
Ya kuma gargadi kwamandoji da su kara kaimi da amfani da cikakken aiki da bayanan leƙen asiri, inda ya ce:
“Ku yi amfani da bayanan sirri don gudanar da ayyukan da suka dogara da leƙen asiri.
"Sun saba kai hari a wuraren da suke ganin ba su da kariya. Idan sun san kuna wurin, ba za su zo ba. Kuma idan suka zo, za ku iya kayar da su, ko ba haka ba?”
Shaibu ya tunatar da jami’an cewa nasara a irin wannan aiki ba wai kawai kare martabar runduna ba ce, har ila yau abu ne da ya shafi ceto rayuka da kuma kare kasa.
Sojoji za su hada kai da 'yan banga
Bayan ganawarsa da sojoji, Laftanar Janar Shaibu ya yi wata tattaunawa ta musamman da ‘yan sa-kai da masu farauta da ke taimaka wa dakarun wajen kai samame cikin dazuka.
Ya yaba musu bisa jarumtaka, yana mai cewa wahalar da suke sha wajen aikin tsaro ba za ta tafi a banza ba.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Idan muna da mutane kamar ku, za ku yi aiki tare da mu, ku ba mu bayanan yankunan da kuka sani.
"Kun san wadannan dazuka, kun san hanyoyi, kuma ku ne za ku gaya mana inda miyagu suke.”
Legit ta tattauna da Muhammad
A tattaunawa da Legit, Hausa, Muhammad Ibrahim da ya ke bibiyan lamuran tsaro ya bayyana cewa zuwan shugaban sojoi Kebbi zai iya yin fa'aida:
"Zuwan shi zai taimaka matukar za a ba dakaru umarnin bin diddigin 'yan ta'adda su ceto daliban.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Sojojin da suka je ceto ɗaliban Kebbi sun faɗa tarkon ƴan bindiga
"Amma matukar irin abin da aka saba ne, babu wani sauyi da za a gani a kasa."
An kashe shugaban MSSN a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa masu garkuwa da mutane sun yi wa wani shugaban kungiyar MSSN kisan gilla a Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwan sun kama Malam Alkasim Ibrahim ne a gonarsa suka kashe shi daga baya.
Farfesa Mansur Sokoto na cikin malaman da suka yi Allah wadai da kisan gillan tare da kira a dauki matakin gaggawa kan rashin tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
