Sarkin Musulmi Ya Mika Bukatarsa ga Jami'an Tsaro kan 'Yan Ta'adda
- Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a wasu sassa daban-daban na kasar nan
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa babu wani kisan kare dangi da ake yi wa mabiya addinin Kirista Najeriya
- Hakazalika, Sultan ya bukaci jami'an tsaro da su nunawa 'yan ta'adda ba sani ba sabo ba tare da la'akari da addini ko kabilarsu ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar Kolin harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro.
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga hukumomin tsaro da su hukunta masu aikata laifi ba tare da kallon addininsu ko kabilarsu ba.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa ya yi wannan kira ne yayin babban taron kungiyar Muslim Ummah of South West Nigeria (MUSWEN) karo na 10, da aka gudanar a dakin taro na Bola Babalakin, Gbongan, jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Sarkin Musulmi ya ce kan kashe-kashe?
Sarkin Musulmi ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke yi a sassan kasar nan.
“An dade ana ta surutai kan kisan kare-dangi, amma na faɗa kuma zan ci gaba da faɗa: ban taɓa ganin an hana wani Kirista 'yancinsa na yin bauta ba.”
“Muna zaman lafiya, ba za mu yarda wani ya raba mu ba. Ka da mu zage mu hukunta mutane bisa zato. A matsayinmu na Musulmai abin da ya kamata shi ne mu zama wadanda za a yi koyi da su."
- Alhaji Muhammad Sa'ad III
Sarkin Musulmi ya ce miyagu ke kashe mutane
Sarkin Musulmin ya jaddada cewa masu kashe jama'a ba Musulmai ba ne, amma miyagu ne, kuma ya bukaci jami’an tsaro da su kama su tare da hukunta su ba tare da la’akari da addininsu ko kabilarsu ba.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su yi addu’a ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni, domin Allah ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya yaba wa MUSWEN bisa kasancewa wata cibiyar haɗin kai da tattaunawa a tsakanin Musulmai na yankin Kudu maso Yamma, yana mai kiran sauran yankuna su yi koyi da su.
A yayin taron, an ba da guraben tallafin karatu ga dalibai mata 12 masu karantar aikin likitanci daga jihohin yankin Kudu maso Yamma.
Shugaba Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfama sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sarkin Musulmin ya yi zama da Mai girma Bola Tinubu ne a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ganawarsu na cikin jerin tattaunawa da neman shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabannin addini da na gargajiya a Najeriya kan barazanar da Amurka ta yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

