Gwamnatin Tinubu Ta Daukarwa 'Yan Najeriya Alkawari kan Sace Dalibai Mata a Kebbi
- Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wata makarantar sakandiren kwana inda suka yi awon gaba da dalibai mata a jihar Kebbi
- Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Mai girma Bola Ahmed Tinubu, ta bayyana harin a matsayin abin takaici kuma rashin imani
- Ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya, yayin da ta bayyana matakan da ta dauka don ganin an ceto daliban cikin koshin lafiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi magana kan dalibai matan da 'yan bindiga suka sace a jihar Kebbi.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta ceto dalibai mata na makarantar sakandire ta GGSS, Maga, da aka sace a karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi.

Source: Twitter
Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 17 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi aika-aika a Kebbi
'Yan bindiga dai sun kai hari a makarantar sakandiren ne inda suka hallaka mataimakin shugaban makarantar.
Hakazalika, 'yan bindigan wadanda suka kai harin a kan babura, sun kuma yi awon gaba da wasu dalibai mata na makarantar.
Me gwamnati ta ce kan sace dalibai matan?
Mohammed Idris ya ce gwamnati na cikin damuwa matuƙa game da lamarin, tana tausayawa iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa tana yin duk mai yiwuwa domin dawo da daliban cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan
Atiku ya kausasa harshe kan sace dalibai mata a Kebbi, ya gwamnatin Tinubu shawara
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa kare rayukan ’yan Najeriya, musamman yara masu zuwa makaranta, babban nauyi ne da ke kan gwamnati."
- Mohammed Idris
Ministan ya yi Allah-wadai da harin, wanda ya bayyana a matsayin abin takaici da rashin imani, ya kuma ce an ba hukumomin tsaro da na leken asiri umurni kai tsaye da su gano inda daliban suke tare da ceto su cikin gaggawa.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun dawo da daliban cikin lafiya kuma mun tabbatar da cewa masu aikata wannan laifi sun fuskanci hukunci.”
- Mohammed Idris

Source: UGC
Gwamnati za ta dauki mataki
Dangane da daukar matakan rigakafi saboda gaba, Mohammed Idris ya ce karfafa tsaron cikin gida na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatin tarayya a yanzu.
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na kara karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninta da kungiyoyin ECOWAS, AU da rundunar kasa da kasa ta MNJTF domin tsare iyakokin kasar nan da dakile ayyukan 'yan ta"adda.
Atiku ya yi tir da sace daliban Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah da sace dalibai mata da 'yan bindiga suka yi a jihar Kebbi.
Atiku ya sace daliban na kara nuna yadda tsaro yake tabarbarewa a kasar nan, wanda a cewarsa hakan ba abin da za a amince da shi ba ne.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen kre rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

