Atiku Ya Kausasa Harshe kan Sace Dalibai Mata a Kebbi, Ya Ba Gwamnatin Tinubu Shawara
- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi martani kan harin ta'addancin da 'yan bindiga suka kai a jihar Kebbi
- Atiku Abubakar ya bayyana harin na 'yan bindigan wanda ya yi sanadiyyar sace dalibai a matsayin abin takaici
- Ya ba gwamnatin tarayya shawarar matakin da ya kamata ta dauka wajen magance matsalar rashin tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a makarantar sakandire ta GGCSS, Maga, a jihar Kebbi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake fasalin tsaron kasa cikin gaggawa.

Source: Facebook
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Atiku ya ce kan sace dalibai mata?

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta daukarwa 'yan Najeriya alkawari kan sace dalibai mata a Kebbi
Atiku ya ce ya ji takaici sosai kan labarin kisan mataimakin shugaban makarantar da kuma sace dalibai da dama, yana mai kiran lamarin a matsayin sabon tabbaci na lalacewar tsaron Najeriya.
“Na gigice da labarin wannan mummunan hari da aka kai GGCSS Maga a Kebbi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mataimakin shugaban makarantar tare da sace daliban da ba su ji ba, ba su gani ba."
"Wannan wata sabuwar tunatarwa ce ta tabarbarewar tsaro a kasarmu."
- Atiku Abubakar
Ya kuma yi Allah-wadai da kisan jigon APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen mutane da dimbin jama’a a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
“Wadannan ta’asar ba su da wurin zama a cikin al’umma mai wayewa."
- Atiku Abubakar
Atiku ya koka kan rashin tsaro
Atiku ya ce irin wadannan tashin hankula da ke faruwa a jihohin Plateau, Benue da wasu sassan kasar, suna barin al’umma cikin fargaba da rudani.
Ya kuma yi nuni da halin da ake ciki a karamar hukumar Shanono ta Kano, inda mutane ke gudun hijira saboda barazanar ‘yan bindiga, yana mai cewa matsalar tsaro ta kai wani mataki da ba za a iya jurewa ba.
“Ba za mu ci gaba da tafiya a haka ba."
- Atiku Abubakar

Source: Facebook
Wace shawara Atiku ya ba gwamnati?
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi gyaran gaggawa a tsarin tsaro, ta kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake fuskantar hare-hare, tare da kafa ayyukan leƙen asiri masu karfi.
“’Yan ƙasa na da hakkin samun kariya, mutunci da zaman lafiya, ba wani abu kasa da haka ba."
- Atiku Abubakar
Ya kara da cewa kare rayukan jama’a shi ne babban alhakin kowace gwamnati, kuma babu wata kasa da za ta samu ci gaba matuƙar ’yan kasarta na rayuwa cikin tsoron tashin hankali da kashe-kashe.
Matawalle ya yi Allah wadai da harin Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi Allah da harin da 'yan bindiga suka kai a wata makarantar sakandire da ke jihar Kebbi.
Matawalle ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomin tsaro umarnin ceto daliban da aka sace.

Kara karanta wannan
Kebbi: Ƴan bindiga sun kai hari makarantar kwana, sun sace dalibai mata masu yawa
Hakazalika, ya kwantar da hankalin jama'a da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin kubutar da daliban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
