A Karo na 7 a Jere, Hauhawar Farashin Abinci da Sauran Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya

A Karo na 7 a Jere, Hauhawar Farashin Abinci da Sauran Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya

  • Hukumar kididdiga ta kasa watau NBS ta fitar da alkaluman hauhawan farashin kayayyaki a Najeriya na watan Oktoba da ya gabata
  • Alkaluman sun nuna cewa hauhawan farashin ya sauka zuwa 16.05% a watan Oktoba, 2025 idan aka kwatanta da na watan Satumba
  • Hakan na nuna cewa jama'ar Najeriya na ci gaba da samun saukin tsadar kayan abinci da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum a kasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Alkaluman kididdiga sun nuna cewa farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na ci gaba da faduwa kasa warwas a kasuwannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Naira tiriliyan 1.4 sun yi ƙafa a CBN, an taso gwamnan babban banki ya yi bayani

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta tabbatar da hakan a rahoton hauhawan farashin kayayyaki da ta fitar na watan Oktoba, 2025.

Kayan abinci a kasuwa.
Hoton wasu kayayyakin abinci a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

NBS ta saki alkaluman hauhawar farashi

A rahoton tashar Channels tv, NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sauka zuwa kashi 16.05 a watan Oktoba 2025 daga kashi 18.02 da aka samu a Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Consumer Price Index (CPI) na watan Oktoba ya nuna cewa an samu raguwar kaso 1.96 daga adadin da aka samu a watan da ya gabata.

Wannan na nuna cewa Najeriya ta jera watanni bakwai a jere tana samun raguwar hauhawar farashi tun daga watan Afrilu 2025.

A ma’aunin shekara-da-shekara, adadin hauhawar farashin ya yi kasa da 17.82% idan aka kwatanta da Oktoba 2024, wanda a wancan lokaci ya kai 33.88%.

Hauhawar farashin kayan abinci

A bangaren abinci, rahoton NBS ya nuna cewa hauhawar farashin abinci a watan Oktoba 2025 ya sauka zuwa 13.12%, ma'ana dai an samu raguwar kaso 26.04 daga na Oktoba, 2024 (39.16%).

Rahoton ya kuma bayyana cewa wannan gagarumin saukin da aka samu ya samo asali ne daga sauya ma'aunin shekara da ake amfani da shi wajen lissafin kididdigar hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun karya farashi, ana sayar da kayan abinci da araha a jihar Benue

Sai dai a ma’aunin wata-wata, rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci ya tashi zuwa -0.37% a watan Oktoba 2025, inda ya karu da kaso 1.21 idan aka kwatanta da na watan Satumba 2025 (-1.57%).

A taƙaice, Najeriya ta samu sauki a lissafin shekara-da-shekara, inda alkaluman hauhawar farashi ya ragu da kashi 17.82% idan aka kwatanta da watanni 12 da suka gabata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Bola Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock da na wasu kayayyaki da ake sayarwa a kasuwa Hoto: @aonanuga1956
Source: UGC

Farashin abinci ya yi warwas a Benuwai

A wani labarin, kun ji cewa mazauna Makurdi, babban birnin jihar Benuwai sun cika da farin ciki yayin da farashin kayan abinci ya kara araha sosai a kasuwanni.

A wata tattaunawa da aka yi da mutane musamman maginta a Makurdi, sun bayyana cewa saukin da aka samu a farashin kayan abinci ya taimaka matuka wajen sauke nauyin gidajensu.

Onyemowo Ejeh, wata 'yar kasuwa, ta ce tana ci gaba da yin asara, domin ta sayi buhun wake mai nauyin 50kg a kan N120,000 a Disambar 2024, amma yanzu ana sayar da shi N85,000.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262