Hukumar kididdiga ta fitar da sabon alkaluman adadin 'yan Najeriya dake kwana da yunwa
- Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewar adadin 'yan Najeriya dake kwana cikin yunwa ya karu matuka
- NBS ta bayyana cewar yanzu haka adadin 'yan Najeriya dake kwana da yunwar ya karu ya zuwa fiye da mutum miliyan 36
- Wani masanin tattalin arziki na kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ya ambaci alkaluman da hukumar ta fitar a Abuja
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewar akwai 'yan Najeriya fiye da mutum miliyan 36 dake kwana da yunwa.
Hukumar NBS ta ce adadin na karuwa ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen kaddamar da tsare-tsare da zasu bunkasa harkar noma.
Wani masanin tattalin arziki na kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), Dakta Manson Nwafor, ya bayyana adadin mutanen dake kwana da yunwa kamar yadda NBS ta fitar.
Nwafor ya bayyana hakan ne yayin halartar wani taro da wata kungiyar 'yan kasuwa ta gudanar a Abuja.
KARANTA WANNAN: An hallaka wata shu’umar dabba dake cin mutane da dabbobi a jihar Kano, duba hotunan ta
Masanin tattalin arzikin ya ce Najeriya ta gaza samun maki mafi karanci na 3.9 cikin 10 a bangaren kaddamar da wasu shirye-shirye a bangaren noma da kungiyar ECOWAS ya fitar.
Dakta Nwafor ya bayyana takaicinsa a kan wannan koma baya da Najeriya ke samu ta fuskar inganta noma domin magance matsalar karancin abinci ga jama'ar kasar ta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng