'Sun Tafka Ta'asa,' An Gano Adadin Dalibai Mata da Ƴan Bindiga Suka Sace a Kebbi

'Sun Tafka Ta'asa,' An Gano Adadin Dalibai Mata da Ƴan Bindiga Suka Sace a Kebbi

  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai hari makarantar mata ta GGCSS Maga, da ke jihar Kebbi
  • Kakakin 'yan sanda na Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya ce yanzu haka 'yan sanda, sojoji, da 'yan sanda sun bazama daji
  • Yayin da jami'an tsaro ke kokarin kubutar da dalibai matan da aka sace, gwamnatin Kebbi ta dauki mataki a nata bangaren

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da sace dalibai mata a makarantar sakandaren gwamnati ta GGCSS, Maga, jihar Kebbi.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan bindiga sun farmaki GGCSS a daren ranar Ladi, inda suka sace dalibai mata masu yawa.

'Yan bindiga sun sace dalibai mata 25 a jihar Kebbi.
Hoton jami'an 'yan sanda suna rangadi a lokacin zaben gwamnan jihar Edo. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kakakin 'yan sandan Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar a shafin rundunar na X a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta daukarwa 'yan Najeriya alkawari kan sace dalibai mata a Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin 'yan bindiga a makarantar Kebbi

Sanarwar ta bayyana cewa:

"A ranar 17 ga Nuwamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na safiya, rahoto ya nuna cewa wasu gungun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari Kebbi.
"Rahoto ya nuna sun bude wuta kan mai uwa da wabi, suka kutsa cikin makarantar sakandaren gwamnati ta mata da ke Maga, gundumar Danko, karamar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar."

Sanarwar ta ce 'yan sandan da ke gadin makarantar, sun yi kokarin dakile harin 'yan bindigar, amma hakan ya ci tura.

"Abin bakin ciki, 'yan bindigar sun tsallake ta katanga, suka shiga cikin makarantar, inda suka sace dalibai 25 daga dakunan kwanansu, suka tafi da su wani wuri da ba a sani ba."

- CSP Nafiu Abubakar.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa 'yan bindigar sun harbe wani Hassan Makaku har lahira, kuma suka ji wa wani Ali Shehu rauni a hannun dama.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kashe mataimakin shugaban APC, 'yan sanda sun dauki mataki

Sojoji, 'yan sanda sun fita neman daliban Kebbi

Bayan samun wannna rahoto, sanarwar ta ce an hada tawagar sojoji, 'yan sanda na musamman, da 'yan sa kai zuwa inda abin ya faru.

Sanarwar ta ce yanzu haka wadannan jami'an tsaron hadin gwiwa na bin sahun 'yan ta'addar, suna duba dazuzzuka domin kubutar da daliban da aka sace, da kuma kama miyagun.

"A bisa wannan mummunan abun da ya faru, kwamishinan 'yan sandan Kebbi, CP Bello M Sani ya ba da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da dagewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar."

- CSP Nafiu Abubakar.

An rahoto cewa Gwamna Nasir Idris ba ya cikin Kebbi lokacin da aka sace daliban makarantar mata.
Hoton gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris a wani taro a Birnin Kebbi. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Facebook

Gwamnatin Kebbi ta dauki matakin gaggawa

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar, sakataren watsa labaran gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, ya bayyana cewa mataimakin gwamna, Sanata Umar Tafida, ya isa makarantar domin duba halin da ake ciki, a madadin gwamnan, wanda ba ya cikin jihar yanzu.

"Yanzu haka mataimakin gwamna yana hanyar zuwa makarantar domin sanin halin da ake ciki. Gwamna ba ya jihar yanzu, amma mataimakinsa zai je a madadinsa.

Kara karanta wannan

Matawalle: Ministan tsaro ya yi martani kan sace dalibai mata a Kebbi

"Gwamna Nasir Idris na hanyar dawowarsa jihar domin duk inda yake, hankalinsa na kan abun da ya faru a wannan makaranta."

- Ahmed Idris.

A baya bayan nan, garin Maga, wanda ke cikin karamar hukumar Danko/Wasagu, ya fuskanci hare-haren 'yan bindiga.

Matawalle ya yi martani kan sace daliban Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya fito ya yi magana kan harin da 'yan bindiga suka kai a makarantar Kebbi.

Matawalle ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindigan suka kai wanda ya jawo hallaka mataimakin shugaban makarantar da ke karamar hukumar Danko/Wasagu.

Karamin ministan ya bayyana umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba hukumomin tsaro kan sace daliban mata da 'yan bindigan suka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com