Yadda 'Yan ISWAP Suka Sake Kama Kwamandan Sojoji, Sun Hallaka Janar a Borno
- Wasu sababbin rahotanni sun tabbatar da cewa Babban Kwamandan Rundunar Damboa, Janar M. Uba, ya rasu a hannun mayaƙan ISWAP
- Bidiyon da ya yi kafin sake kama shi ya nuna cewa yana cikin koshin lafiya, amma daga baya ya bace a dajin a hanyarsa ta dawo wa barikin sojoji
- Dakarun ƙasa da na sama sun yi ƙoƙarin ceto shi, amma an sake kama shi bayan rahoton cewa an sace shi ya yadu a kafafen yada labarai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Rahotanni sun tabbatar da cewa Janar M Uba, Kwamandan Runduna na Damboa, ya rasu bayan harin da mayaƙan ISWAP suka kai.
Da fari, an rika yada labarin cewa mayakan ISWAP sun kama jagoran sojoji, amma daga bisani ya fitar da bidiyo, inda ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa sai dai bayan wasu awanni a cikin daji ya rasa hanyar komawa sansaninsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe jagoran sojoji
Dakarun soji—na ƙasa da na sama—sun yi ta ƙoƙarin ceto shi bayan ya shaida musu cewa yana kan hanyarsa ta komawa sansani.
Amma abin takaici, an sake kama shi daga baya, bayan rahoton sacewarsa ya bazu a kafafen sada zumunta.

Source: Twitter
Sababin rahotannin da ke yawo sun tabbatar da cewa an kashe shi bayan mayakan ISWAP sun kama shi a karo na biyu.
Labarin ya girgiza mutane da dama, musanman ganin girman jami'in sojin da yadda aka samu labarin cewa lafiyarsa kalau kafin a sake kama shi.
Jama'a sun yi ta'aziyyar sojan
Wasu mutane daga cikin masu bibiyar shafin sun miƙa ta'aziyya kan rasuwar, inda suka bayyana takaici kan kisan babban jami'in sojan.
@UmarAdamuBello4 ta ce:
“Allah ya jikan shi, ya saka masa da aljanna bisa sadaukarwar da ya yi wa ƙasarsa.".

Kara karanta wannan
An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP
@Saifull74385178 ya ce:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya yi masa rahama. Allah Ya gafarta masa duka zunubansa."
@BidemiSugar
"Dama shi suka yi niyyar kashewa. Babu abin da za a fada min bayan wannan."
Labarin rasuwar babban jami'in sojan ya zo wa mutane da dama da mamaki, musamman bayan an sanar da cewa lafiyarsa ƙalau da fari.
Har yanzu rundunar tsaron kasar nan ba ce komai a kan sabon labarin rasuwar babban jami'in ba , musamman bayan ƙaryata labarin cewa an kama shi da fari.
Sojoji sun yi wa ISWAP kwantan bauna
A baya, mun wallafa cewa Najeriya karkashin Operation Hadin Kai ta samu nasarar gudanar da kwanton bauna ga mayakan ISWAP a yankin Banki na jihar Borno.
Majiyoyi sun ce aikin ya faru ne a daren 13 zuwa safiyar 14 ga Nuwamba, 2025 a lokacin da ‘yan ta’addan ke kan babura dauke da makamai don kai hari.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ba a samu asarar rayuka a ɓangaren sojoji, kuma babu wata na’urarsu da aka rasa a lokacin wannan farmaki da sojoji suka yi nasara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

