Sule Lamido Ya Fadi Matsayarsa kan Taron PDP da Ya Nemi Kotu Ta Dakatar

Sule Lamido Ya Fadi Matsayarsa kan Taron PDP da Ya Nemi Kotu Ta Dakatar

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce taron da aka gudanar a Ibadan ba taron ƙasa na PDP ba ne face taron nishadi kawai
  • Sule ya zargi jami’an PDP da karya doka bayan kotu ta dakatar da gudanar da taron kafin a bayan ya shigar da kara yana kalubalantarsa
  • A wannan taro da Sule Lamido ya ce bai halatta ba, an zabi sabon shugaban PDP, Kabiru Turaki, duk da adawar wasu daga cikin 'yan jam'iyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma jagora a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya kwatanta taron zaben shugabanni da aka yi a Ibadan a ranar Asabar da wani taron nishadi.

Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, bayan PDP ta hana shi damar sayen takardar tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Saraki da wasu kusoshin PDP da suka ki halartar babban taron jam'iyyar a Ibadan

Sule Lamido ya yi fatali da taron PDP
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamdio Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Sule Lamido ya ce taron ya saba ka’ida ganin cewa kotu ta taka wa taron burki, amma suka yi gaban kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya soki taron PDP

Premium Times ta wallafa cewa Sule Lamido ya bayyana takaici a kan yadda wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa suka bijirewa umarnin kotu.

A cewarsa:

“PDP jam’iyya ce ta doka da oda. Abin da aka yi a Ibadan ba taron ƙasa ba ne. Mutane ne kawai suka taru don nishadantar da kansu.”

Sule Lamido, wanda ya taba zama ministan harkokin wajen Najeriya, ya kai ƙara gaban kotu bayan an hana shi sayen fom ɗin takara.

A ranar 11 ga Nuwamba, Alkali Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya dakatar da taron, tare da umartar INEC kada ta amince da shi.

Rikici ya balle a jam'iyyar PDP

Kafin karar da Sule Lamido ya shigar, wasu jagororin Arewa sun goyi bayan Kabiru Turaki a matsayin ɗan takarar shugabancin jam’iyya, amma Sule Lamido ya yi watsi da hakan.

Kara karanta wannan

An samu rudani yayin da PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyya na kasa a taron Ibadan

Sule Lamido ya ce kotu ta hana taron PDP
Jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido Hoto: Sule Lamdio
Source: Facebook

A ranar 14 ga Nuwamba, sa’o’i kaɗan kafin taron, kotu ta sake bada umarnin dakatar da shi har sai an ba Sule Lamido damar tsaya wa takara.

Duk da haka, jam’iyyar ƙarƙashin Umar Damagum ta ci gaba da taron, inda a nan ne aka Nyesom Wike, Ayodele Fayose, sakatare na ƙasa Samuel Anyanwu da wasu mutum takwas.

A taron ne kuma aka zabi Kabiru Turaki a matsayin sabon shugaban ƙasa na PDP duk da adawa da wasu 'yan jama'iyya ke yi da hakan.

PDP ta rikice bayan korar Wike

A baya, mun ruwaito cewa PDP ta shiga sabon rikicin cikin gida, bayan da wasu daga cikin manyan jam'iyya suka nesanta kansu da korar Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi gaggawar nesanta kansa da korar, inda ya bayyana cewa matakin ba zai taimaka wajen samar da hadin kai a cikin PDP ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas

Hakanan, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa ba a tattauna batun korar Wike da sauran mutane bakwai da aka sallama a taron gwamnonin PDP ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng