Mansur Sokoto Ya Fadi yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Shugaban MSSN a Kebbi

Mansur Sokoto Ya Fadi yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Shugaban MSSN a Kebbi

  • An kashe Ustaz Al-Qasim Ibrahim Amir na MSSN a Kebbi bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi a gonarsa
  • Farfesa Mansur Sokoto ya tabbatar da kisan Usman Ibrahim tare da roƙon a guji yada hotonsa saboda muninsa
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi tir da al’amarin, suna kira ga addu’a da ɗaukar matakin da ya dace kan 'yan ta'adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Rikicin tsaro a yankin Arewa maso Yamma ya sake ƙara ta’azzara yayin da ’yan bindiga suka kashe shugaban MSSN na Yauri a jihar Kebbi, Ustaz Al-Qasim Usman Ibrahim.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan sace shi daga gonarsa da maraice.

Alkasim Ibrahim Usman da aka kashe
Shugaban MSSN da 'yan bindiga suka kashe a Kebbi. Hoto: Katsina Post News
Source: Facebook

Farfesa Mansur Sokoto ya tabbatar da rasuwar shugaban cikin alhini a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka afka wa mazauna Zamfara, sun kwashe sama da mutum 60

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan aukuwar lamarin, jama’a daga sassa daban-daban sun yi ta mika sakonnin ta’aziyya da addu’o’i, tare da zafafa kira ga gwamnati da hukumomi da su ɗauki matakai masu ƙarfi.

Sanarwar da Farfesa Mansur Sokoto ya fitar

Farfesa Mansur Sokoto ya sanar da cewa an aiko musu da hoton marigayin bayan kashe shi, sai dai ya nemi jama’a da su guji yada hoton saboda tsananin muni da kuma girmama mamacin.

Malamin ya ce:

“Yau kuma a Kebbi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
"Ɗan uwa Ustadh Al-Qasim Usman Ibrahim Amir na MSSN Yauri da aka yi garkuwa da shi daga gonarsa a yau da maraice, an turo hotonsa bayan kisan gila da ’yan ta’addan suka yi masa.
"Ba na iya ɗaura hoton, kuma ina roƙon don Allah kada wanda ya ɗaura shi. Idan ma wani ya ɗaura ya cire shi.”

Ya ci gaba da cewa:

“’Yan uwa mu dage ga roƙon Allah ya shiga cikin lamarinmu ya ɗauke mana fitinar waɗannan fitinannun.

Kara karanta wannan

Turaki: PDP ta zabi sabon shugaban jam'iyyar, ya fadi yadda zai kawo sauyi

Allah ya isar mana, ya yi mummunar damƙa a kan masu ta’addancin nan da masu ɗaure masu gindi da masu taimakon su ta kowace hanya.
"Allah ya jiƙan Ustadh Al-Qasim, ya karɓe shi cikin shahidai. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.”

Sakon ta’aziyya da addu’o’in al’umma

Bayan fitowar labarin, mutane da dama sun nuna alhininsu a kafafen sada zumunta, Mubarak Abdullahi ya ce:

*“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya jiƙansa da rahama, ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.”

Aliyu Ahmad Danmanga ya yi addu’a da cewa:

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa, ya sa mutuwa ta zamo hutu gare shi. Allah ka amintar da mu ka ba mu zaman lafiya. Allah ka isar masa.”

Mallam Imrana ya bayyana cewa:

“Allah ya gafarta masa. Abubuwan dai sai da addu’a. Ba mu da wani abu da ya fi hakan; masu makaman yaƙi sun gaza.”
'Yan bindiga a Katsina
'Yan bindiga yayin wani zaman sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

An bindige matashi wajen jana'iza

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargi 'yan kungiyar asiri ne sun kai hari wani wajen da ake jana'iza a Cross River.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi da ake jana'izar mahaifinsa bayan sun bude masa wuta.

Bayan kashe matashin, mutanen sun yi wa wata mata rauni da bindiga kuma a halin yanzu tana asibiti tana karbar magani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng