Da Gaske An Yi Yunkurin Kashe Laftanal Yerima a Abuja? An Ji Ta Bakin 'Yan Sanda
- Rundunar 'yan sanda ta warware rudanin da aka samu game da zargin yunkurin kashe Laftanal A.M Yerima a cikin Abuja
- SP Josephine Adeh, kakakin 'yan sandan Abuja, ta ce babu wani yunkuri na kashe sojan da ya yi cacar baki da Nyesom Wike
- Idan ba a manta ba, Yerima ne ya hana ministan Abuja da tawagarsa ta hukumar FCDA shiga wani fili da ke a gundumar Gaduwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta karyata rahotannin da ke yawo cewa an kai hari kan sojan ruwa da ya yi cacar baki da Nyesom Wike.
Legit Hausa ta rahoto cewa, Laftanal A.M Yerima, shi ne sojan ruwa da ya yi sa'in'sa da ministan Abuja, Nyesom Wike a wani fili a birnin tarayya.

Kara karanta wannan
An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP

Source: Twitter
Sanarwar da SP Josephine Adeh, kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, da aka wallafa a shafin rundunar na X, ta ce babu wani yunkuri na hallaka A.M Yerima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin yunkurin kashe Laftanal Yerima
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan labari ya yadu a shafukan sada zumunta cewa Laftanal Yerima ya tsallake rijiya ta baya-baya a harin da aka kai masa.
Rahoton, wanda 'yan sanda suka kira na karya, ya ce wasu mutane sanye da bakaken kaya, a cikin motocin Hilux biyu ne suka yi yunkurin kashe sojan.
An ce, mutanen sun bi Yerima a cikin motar da yake, inda suka fara 'yar tsere da shi tun karfe 6:30 na yamma a gidan man NIPCO da ke hanyar Kubwa har zuwa hanyar Gado Nasco.
Rahotannin sun nuna cewa, sojan ruwan ya yi nasarar tserwa miyagun da ke bin sa ne bayan dogon lokaci suna tsere, kamar yadda muka rahoto.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun ga ta kansu: Hafsan sojojin sama ya sha alwashi kan rashin tsaro
Har ma ana zargin cewa, yunkurin kashe Yerima na da alaka da takawa Wike burki da sojan da ya yi, lokacin da ya je kwace filin da suke gadi a cikin Abuja.
'Babu yunkurin kashe sojan ruwan' - 'Yan sanda
To amma, a sanarwar da 'yan sanda suka fitar a daren Lahadi, SP Josephine ta ce dukkan wannan labarin, kanzon kurege ne.

Source: Twitter
SP Josephine ta sanar da cewa, babu wani rahoto makamancin wannan da aka kawo ofishin rundunar, kuma ba su ji labarin faruwar makamancin haka ba a Abuja.
Sanarwar ta ce:
"Muna so mu sanar da al'umma cewa babu wani yunkuri na kashe Laftanal Ahmed Yerima, domin ba a kawo mana rahoton faruwar hakan a Abuja ba.
"Muna shawartar jama'a da su yi watsi da wannan rahoton karyar, kuma su guji yada labaran da ba a tantance ba, don gudun jefa fargaba a zukatan mutane."
Kakakin rundunar 'yan sandan ta kuma bukaci al'umma da su zamo masu sa ido a yankunansu, su kuma kai rahoton duk wani abun da basu yarda da shi ba ga ofishin 'yan sanda mafi kusa.
Wike ya kare kansa bayan rigima da soja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kare rigimar da ya yi da wani jami’in sojan ruwa kan filin da tsohon hafsan ruwa ke ikirari.
Nyesom Wike ya ce ba zai zauna a ofis ba yana kallo jami’an gwamnati suna fuskantar cin zarafi ba yayin gudanar da aikinsu na hukuma.
Ministan Abujan ya kara da cewa ba ya da matsala da rundunar soji, sai dai yana kare doka daga masu amfani da karfin soja don tauye gaskiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
