Amurka za Ta Fara Cikakken Bincike kan Najeriya game da Zargin Kisan Kiristoci

Amurka za Ta Fara Cikakken Bincike kan Najeriya game da Zargin Kisan Kiristoci

  • Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zaman sauraro kan matakin da Donald Trump ya ɗauka na sanya Najeriya a CPC
  • Zaman zai tattauna yiwuwar takunkumi da matakan siyasa kan zargin cin zarafin 'yancin addini a Najeriya da Trump ya yi
  • Shugaba Bola Tinubu ya karyata zargin kashe Kiristoci yana mai cewa hakan ba ya nuna ainihin tsarin da Najeriya ke kai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilan Amurka ta sanar da shirinta na gudanar da wani zama na musamman a ranar 20, Nuwamba, 2025 a kan Najeriya.

Za a yi zaman ne domin nazari kan sababbin zarge-zargen kisan gilla da cin zarafin 'yancin addini a Najeriya.

Donald Trump tare da Bola Tinubu
Donald Trump na Amurka tare da shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|The White House
Source: Getty Images

Punch ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan matakin shugaba Donald Trump na sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take hakkokin addini (CPC).

Kara karanta wannan

Fafaroma Leo ya sanya Najeriya a cikin kasashen da ake tsananta wa kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Amurka za ta yi zama kan Najeriya

A cewar bayanan da aka tura wa ‘yan kwamitin harkokin kasashen waje, zaman zai gudana da ƙarfe 11:00 na safe a dakin Rayburn 2172, an ce zai kasance a buɗe tare da watsa shi kai tsaye.

Wannan mataki ya sake tayar da muhawara mai zafi kan yawaitar hare-haren da ake alakantawa da rikicin addini a Najeriya.

Bayanan gayyata sun nuna cewa za a gabatar da shaidu daga jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka da wasu shugabannin addini na Najeriya, domin fayyace yanayin da ake ciki.

Wadanda Amurka ta gayyata zaman

A cikin gayyatar da aka rabawa ‘yan kwamitin, an bayyana cewa shaidu za su haɗa da babban jami'i a sashen harkokin Afirka, Jonathan Pratt da Jacob McGee.

Shugabannin addini da za su halarta sun haɗa da Ms Nina Shea, Bishop Wilfred Anagbe na Makurdi, da Ms Oge Onubogu.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana wani jawabi a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kwamitin zai nazarci ko Najeriya ta gaza kare 'yancin addini, tare da duba maganar takunkumi, taimakon jin kai, da haɗin gwiwa da hukumomin Najeriya domin rage tashin hankali.

Kara karanta wannan

DSS ta tafi kotu da wanda ya nemi a yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Zargin da Trump ya yi a Najeriya

A ranar 31, Oktoba, 2025, Trump ya ayyana cewa Najeriya ta shiga CPC saboda “tsananin cin zarafin 'yancin addini.”

Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci “sun shiga barazana,” inda ya ce an kashe dubban Kiristoci ta hannun ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi.

A cikin wata sanarwa mai zafi, ya ce:

“Idan gwamnatin Najeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi. Za mu iya shiga kasar domin kawar da ‘yan ta’adda da ke kai wadannan hare-hare,”

Martanin da Tinubu ya yi ga Trump

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya karyata zargin Donald Trump, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Shugaban ya ce Najeriya ƙasa ce ta dimokuraɗiyya wacce kundinta ya tanadi ‘yancin addini ga kowa da kowa.

Sai dai duk da martanin da Najeriya ta yi, Trump da wasu 'yan majalisar Amurka sun dage da cewa zargin da suka yi gaskiya ne ba tare da gabatar da hujjoji gamsassu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng