Fafaroma Leo Ya Sanya Najeriya a cikin Kasashen da Ake Tsananta wa Kiristoci
- Fafaroma Leo XIV ya bi bayan Donald Trump da wasu ƴan majalisar Amurka a kan halin da kiristoci ke ciki a Najeriya
- Shugaban ɗarikar katolika na duniya ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da Kiristoci ke fuskantar wariya da tsananta wa
- Yana nanata wannan batu ne duk da bayanan gwamnatin Najeriya da na hukumomi masu zaman kansu da ke ƙaryata haka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Vatican City – Fafaroma Leo XIV ya bayyana Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin kasashen da Kiristoci ke fama da wariya da fuskantar tsanani.
Leo XIV, wanda ɗan asalin Amurka ne ya yi kalaman da ke nuna goyon baya ga kalaman Shugaba Donald Trump a kan kiristocin Najeriya.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi yayin da ake ci gaba da tattauna batun kisan kiristoci a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fafaroma ya taso Najeriya a gaba
The Cable ta wallafa cewa Fafaroma Leo XIV ya ce Kiristocin Najeriya na fuskantar kalubale daban-daban saboda addininsu.
Ya kara da cewa zaman lafiya dabi’a ce da dukkanin mutane ya kamata su runguma domin a samu wanzuwar kwanciyar hankali.
A cewarsa:
“A sassa daban-daban na duniya, Kiristoci na fama da wariya, musamman a Bangladesh, Najeriya, Mozambique, Sudan da sauran kasashe da muke ta jin labarin hare-hare kan al’umma da wuraren ibada.”

Source: Facebook
Ya ci gaba da cewa:
"Ina taya iyalan Kivu a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo addu’a, inda aka yi kisan jama’a kwanan nan.”
Fafaroman ya yi kira da cewa a yi addu’a domin a kawo ƙarshen duk wani tashin hankali, kuma mabiya addinai su haɗa kai don ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka
Vatican ta yi magana kan Musulmin Najeriya
Maganganun Fafaroman sun biyo bayan karuwar rahotannin tsananta wa Kiristoci a Najeriya, musamman daga bakin Donald Trump da Amurka.
A bara ne kungiyar Aid to the Church in Need (ACN), wata cibiyar addini ta Vatican, ta fitar da rahoto da ya lissafo Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin kasashe 24 da ake take ‘yancin addini sosai.
Sai dai yayin gabatar da rahoton a Roma, sakataren Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya nuna cewa rikicin Najeriya bai ta'allaka kan addini kacokan ba.
Ya ce:
"Ya kamata mu gane cewa Musulmi da dama a Najeriya su na fuskantar zalunci. Waɗannan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ba sa bambanci wajen kai farmaki ga wadanda suka ɗauka a matsayin abokan gaba.”
Wannan furuci nasa ya haifar da martani mai zafi daga wasu malamai Katolika da suka ce maganarsa na rage tsananin matsalar da Kiristoci ke ciki.
Wannan na zuwa bayan Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya a jerin kasashen da ake damuwa da su musamman (CPC) saboda waɗannan rahotanni.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
Amma gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta hakan, tana mai cewa kasar nan ta bai wa kowa ƴancin gudanar da addininsa.
CAN ta magantu kan kisan kiristoci
A baya, kun ji cewa Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa don kare rayukan Kiristoci da dukiyoyinsu..
CAN ta ce ta dade tana jan hankalin ƙasashen duniya game da 'ta’addancin' da Kiristoci ke fuskanta musamman a wasu sassan Najeriya don a kawo masu ɗauki
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya jaddada cewa hukumomin tsaro da gwamnati su tabbatar da adalci da hukunta waɗanda aka tabbatar da aikata laifi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
