‘Mahaifina Ya Hana Ni Daukar Fansa bayan Kashe Ki’: Dan Tsohon Shugaban Kasa

‘Mahaifina Ya Hana Ni Daukar Fansa bayan Kashe Ki’: Dan Tsohon Shugaban Kasa

  • Thomas Aguiyi-Ironsi ya yi magana game da abin da ya faru a mahaifinsa marigayi Johnson Aguiyi-Ironsi bayan juyin mulki
  • Tsohon ministan ya ce bar komai ga Allah, yana mai cewa Najeriya ta koyi darasi daga abin da ya faru da mahaifinsa
  • Ya bayyana cewa mahaifinsa ya umarce shi ka da ya ɗauki fansa, don haka ba ya rike da wata gaba, yana nan yana bin shawarar da ya bar masa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan marigayi tsohon shugaban kasa, Johnson Auiyi-Ironsi ya yi magana kan juyin mulkin da ya yi ajalin mahaifinsa a Najeriya.

Thomas Aguiyi-Ironsi ya ce abin da ya faru ya faru, ya kamata Najeriya ta koyi darasi daga abubuwan da suka faru ne a kasar.

Dan tsohon shugaban kasa ya ce ba zai dauki fansar kashe mahaifinsa ba
Marigayi Aguiyi-Ironsi da dansa, Thomas. Hoto: HistoryVille, Arise TV.
Source: Facebook

Aguiyi-Ironsi: Darasin da yan Najeriya za su koya

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Sowore ya fadi abin da ya sa ake tsare da malamin, ya sha alwashi

Thomas ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Punch wanda aka wallafa a jiya Asabar 15 ga watan Nuwambar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Thomas ya ce ko kadan bai rike abin a zuciyarsa ba saboda bakin ciki ko damuwa bai haifar da ci gaba a kasa baki daya.

Ya ce wadannan munanan al’amura sun nuna mana cewa haɗin kai ba ya dorewa idan babu adalci, kuma adalci ba zai yiwu ba idan babu gaskiya.

Ya ce:

“Baƙin ciki ba ya haifar da ci gaba. Abin da nake ɗauke da shi shi ne tabbaci cewa dole Najeriya ta koyi darasi daga tarihinta don ka da ta maimaita shi.
"Wadannan mummunan al’amura sun nuna mana cewa haɗin kai ba ya dorewa idan babu adalci, kuma adalci ba zai yiwu ba idan babu gaskiya."
Dan Aguiyi-Ironsi ya fadi wasiyyar da mahaifinsa ya ba shi
Marigayi Aguiyi-Ironsi yayin jawabi ga dakarun sojoji. Hoto: HistoryVille.
Source: Getty Images

Abin da Ironsi ya fadawa dansa kafin rasuwarsa

Thomas ya bayyana abin da mahaifinsa, Aguiyi-Ironsi ya fada masa kafin mai afkuwa ta afku inda ya ce yana ci gaba da yi masa biyayya.

Ya ce dole ne yan Najeriya su mutunta bambance-bambance da ke tsakaninsu kamar yadda Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) ke fada.

Kara karanta wannan

'Ba sani ba sabo': Marwa ya yi magana bayan Tinubu ya sake nada shi shugaban NDLEA

Har ila yau, ya ce ko kadan rike mutum ko abu a zuciya ba shi ne mafita ba kuma hakan matsala zai haifar ba kawo gyara ko maslaha ba.

"Mahaifina ya ce min a Ibadan kafin a tafi da shi ka da in ɗauki fansa. Na yi biyayya ga mahaifina.
"Kamar yadda Sardauna mai girma ya ce, dole mu girmama bambance-bambancenmu, mafi kyawun girmamawa ga duk waɗanda suka rasu a 1966, daga bangarori biyu, ba fansa ba bane, sai gyara da tsari mai inganci.”

- Thomas Aguiyi-Ironsi

Matar marigayi Aguiyi-Ironsi ta rasu

A baya, an ji cewa an shiga jimami bayan samun labarin cewa Allah ya yi wa Victoria, matar tsohon shugaban kasan Nigeria na soji, Aguiyi-Ironsi rasuwa.

Victoria Aguiyi-Ironsi ta rasu ne a ranar Litinin 22 ga watan Agustan 2021 tana da shekaru 97 a duniya bayan fama da jinya.

Marigayi Manja Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya shugabanci Nigeria tsawon wata shida kafin a masa juyin mulki a 1966.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.