Ana cikin Rudani: Wasu Sun Kona Amarya da Uwargida a Gidan Aurensu a Kano

Ana cikin Rudani: Wasu Sun Kona Amarya da Uwargida a Gidan Aurensu a Kano

  • An shiga firgici a Kano bayan wasu da ba a san su ba sun kona matan aure biyu a gidansu, lamarin da ya tayar da hankali a Tudun Yola
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar iftila’in a Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025 lokacin maigidan bai nan
  • Majiyoyi sun ce maharan sun shiga gidan tun kafin dare, yayin da ɗan gidan ya bayyana cewa sun tarar da ɗaya daga cikin matan tana ci da wuta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An shiga cikin rudani da rashin tabbas bayan wasu da ba a san ko su waye ba, sun kona matan aure a cikin gidansu a jihar Kano.

Ana zargin mutanen sun shiga gidan ne tun da rana inda suka zauna har bayan sallar mangariba tare da aiwatar da abin da ya kawo su.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

An kona wasu matan aure 2 a Kano
Kakakin yan sanda a kano. Abdullahi Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

An kona amarya, uwargidanta a Kano

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fadawa BBC Hausa cewa sun kaddamar da bincike kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa iftila'in ya afku ne da rana a ranar Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025 a lokacin da mai gidan ba ya gida.

Majiyoyi suka ce lamarin ya faru a Unguwar Tudun Yola da ke cikin ƙaramar hukumar Gwale, a tsakiyar birnin Kano.

Abubuwan da aka samu a gidan a Kano

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa ba zai yi karin bayani ba domin kauce wa duk wani abu da zai iya shafar binciken da ke gudana.

Kiyawa ya ce jami’ansu sun samu wayoyi biyu da ake kyautata zaton na mutanen da suka aikata laifin ne.

Yan sanda sun fara bincike bayan kona amarya da uwargidanta
Taswirar jihar Kano da ke zama cibiyar kasuwanci a yankin Arewa. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda lamarin ya faru a Kano

Wani na kusa da maigidan ya shaida cewa maharan sun shiga gidan tun kafin dare ya yi, amma hakan bai sa an ankara ba a lokacin.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan shekaru 9, kotu ta yanke wa mutum 4 hukuncin kisan ta hanyar rataya

Anas Sha’aibu, ɗa ga maigidan, ya bayyana cewa yana gida da yamma lokacin da mahaifinsa ya kira shi ya sanar da shi cewa ya hanzarta zuwa gidan, domin gobara ta tashi.

Ya ce:

''Bayan zuwanmu gidan, sai muka tarar da wani abu daban, domin kuwa mun tarar da ɗaya daga cikin matan na ci da wuta, ɗayar kuma ta kulle kanta a ban-ɗaki.''

Ya ce sun yi ta ƙoƙarin buɗe ƙofar banɗakin, kuma bayan dogon yunƙuri ne suka yi nasarar karya sakatar.

“Da muka shiga, sai muka samu gawarta a ciki, ita ma ta riga ta mutu, abin da muka gane shi ne an kunna wuta a kan tabarma, sannan aka tura hayaki ta cikin tagar bandakin."

- Anas Sha’aibu

An kama ma'aurata da zargin kashe dansu

A baya, an ji cewa wasu ma'aurata biyu a jihar Imo sun shiga hannun 'yan sanda bisa zargin halaka dan cikinsu.

Ma'auratan sun kashe dan nasu tare da birne shi a boye saboda baya jin magana kuma kullum cikin daga masu hankali yake.

Kakakin 'yan sandan jihar, CSP Michael Abattam ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya tabbatar da cewa an cafke wadanda ake zargi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.