Jita Jita Ta Kare: Gaskiya Ta Fito game da Labarin Rasuwar Tsohon Gwamna a Najeriya

Jita Jita Ta Kare: Gaskiya Ta Fito game da Labarin Rasuwar Tsohon Gwamna a Najeriya

  • Labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obianu ya mutu ba gaskiya ba ne
  • Jita-jitar wacce ta fara yawo har a kafafen watsa labarai ta yi ikirarin cewa Obiaano ya mutu ne a birnin Landan na kasar Birtaniya
  • Sai dai tsohon kwamishinan yada labarai a Anambra, Don Adinuba ya ce Obiano na nan a raye kuma cikin koshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - A yau Juma'a, 14 ga watan Nuwamba, 2025 ne wani rahoto ya bulla cewa tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya riga mu gidan gaskiya.

Rahoton, wanda ya karade kafafen sada zumunta da wasu gidajen jarudu, ya yi ikirarin cewa Mista Obiano ya mutu ne a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Tsohon gwamna, Obiano.
Hoton tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano Hoto: Willie Obiano
Source: Facebook

Dagaske tsohon gwamnan Anambra ya rasu?

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka zuwa jam'iyyar YPP? Gaskiya ta fito

Amma wani rahoto da The Cable ta kawo, bayanai daga makusantan tsohon gwamnan sun nuna cewa Mista Obiano na nan a raye kuma cikin koshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Anambra, Don Adinuba ya fito ya yi bayani kan wannan jita-jitta, yana mai bayyana cewa ba gaskiya ba ne.

Mista Adinuba ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana nan a raye bai mutu ba, yanzu haka ya yi tafiya zuwa jihar Texas da ke kasar Amurka.

Wane hali Obiano ke ciki a kasar waje?

A wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a, tsohon kwamishinan ya tabbatar wa jama'a cewa Obiano yana cikin koshin lafiya, ƙarfi, kuma yana zaune a jihar Texas ta Amurka.

“Kafafen yada labarai na Najeriya sun cika da jita-jitar cewa tsohon gwamnan Anambra, Chief Willie Obiano, ya rasu a Landan, wannan labari babu kanshin gaskiya.
"Cif Obiano ya na zaune a jihar Texas, Amurka, ba a Landan ba. Sannan ba wai batun yana raye kawai ba, Obiano na cikin ƙoshin lafiya da kuzari fiye da yadda ake zaton mutum mai shekara 70.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

“Sakonnin kauna da damuwa bila adadin da jama’a suka turo mana bayan bullar wannan jita-jita ya nuna irin muhimmancin da Chief Obiano yake da shi a zuciyar mutane."

- Don Adinuba.

Tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Hoton tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano yana daga wa masoya hannu Hoto: Willie Obiano
Source: Facebook

Ya kara da cewa duk da ya kai shekaru 70 a duniya, Obiano ya shiga sahun mutanen da aka taɓa yaɗa jita-jitar rasuwarsu kamar Great Zik na Afirka, wanda daga baya aka tabbatar cewa labarin karya ne tsagwaro.

Ya bukaci yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar rauwar Obiano, yana mai jaddada cewa yana nan a raye kuma cikin koshin lafiya, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

EFCC ta maka Obiano a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra bisa zargin ya karkatar da Naira biliyan hudu lokacin mulkinsa.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya sha alwashin sake duba duk wasu manyan laifuka da aka yi watsi da su.

Tun a shekarar 2022 ne EFCC ta fara kama Mr Obiano a filin jirgin sama yana shirin barin kasar, awanni bayan sauka daga mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262