Abba Kabir Ya Tura 'Yan Kano 350 Karatu India, Ya Musu Wasiyya Mai Ratsa Zuciya

Abba Kabir Ya Tura 'Yan Kano 350 Karatu India, Ya Musu Wasiyya Mai Ratsa Zuciya

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi bankwana da dalibai 350 da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasashen waje
  • Daliban na daga cikin shirin tura mutane 1,001 karatu ketare da jihar ta kaddamar domin gina hazikan matasa
  • Gwamnan ya shawarci daliban su zama jakadu nagari na Kano da Najeriya tare da aiki da ilimin da za su samu ga cigaban jiharsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi bankwana da dalibai 350 da gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunsu domin ci gaba da karatu a kasashen waje.

Wannan na daga cikin manyan bangarorin shirin tallafin karatu da gwamnatin jihar ta kaddamar domin gina basirar matasa.

Kara karanta wannan

Bayan rikicin manoma da makiyaya, gwamnati ta dakatar da sarakuna 2 a Gombe

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf yana bankwana da daliban Kano da za su tafi India. Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook ta bayyana cewa kasar India daliban za su tafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi jawabi ga daliban ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya ja hankalinsu cewa wannan dama da suka samu tana da muhimmanci sosai.

Abba Kabir ya ja hankalin daliban Kano

Abba Kabir Yusuf ya yabawa daliban kan samun wannan dama, yana mai cewa gwamnati ta zuba jari ne cikin iliminsu domin su dawo su ba da gudummawa ga cigaban Kano da Najeriya baki ɗaya.

A cewarsa:

“Ku dauki wannan karatu da muhimmanci. Wannan dama ba wai gata ba ce kawai, nauyi ne da kuke dauke da shi na yin fice a karatu.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya bukaci 'yan jarida su rika adalci da fadin gaskiya kan gwamnatinsa

Ya nuna kwarin gwuiwa cewa ilimi da kwarewar da daliban za su samu a kasashen waje za su taka rawar gani wajen inganta harkokin kimiyya, fasaha, kiwon lafiya da sauran muhimman sassa a jihar.

Wasiyyar Abba ga daliban Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma shawarci daliban da su yi rayuwa mai tsafta da ladabi a kasashen da za su je, domin su wakilci Kano da Najeriya cikin mutunci.

Daily Trust ta rahoto ya ce:

“Ku zama jakadu nagari ga Kano da Najeriya. Ku nuna tarbiyya, ku nuna al’ada da dabi’unmu na kirki a duk inda kuka samu kanku.”

A karshe, gwamnan ya yi addu’ar Allah ya ba su nasara a karatun da suka je tare da musu fatan dawowa lafiya bayan kammalawa.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da wani dalibin da zai tafi India. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Taron bankwanan ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Isma’il Jibril Falgore; sakataren gwamnati, Umar Faruk Ibrahim; da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Dr Suleiman Wali Sani sun hallara.

Sauran wadanda suka halarta sun hada da mambobin majalisar zartarwa ta jihar, wasu jami’an gwamnati da kuma iyayen daliban da suka ci gajiyar shirin.

Kara karanta wannan

Hotunan Abba Kabir da Ganduje sun yi kicibis a karon farko tun bayan zaben 2023, sun yi gaisuwa

Dalilin cigaba da kai hari Kano

A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da samun bayanai kan dalilan da ya sa 'yan bindiga ke kara kakkauta kai hari Kano.

Masana sun bayyana cewa karin matsin lamba da 'yan bindiga ke fuskanta a wasu jihohi na sanya su shiga wasu yankunan Kano.

Wani masani kan harkokin tsaro ya ce sulhu da ake da 'yan bindiga a Katsina da wasu jihohi na cikin abubuwan da ke sanya su hijira.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng