Kano: Bayan Shekaru 9, Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisan Ta Hanyar Rataya

Kano: Bayan Shekaru 9, Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisan Ta Hanyar Rataya

  • Bayan shafe shekaru da dama, wata kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ta rataya ga mutane hudu bisa zargin kisan kai a jihar
  • Ana zargin wadanda aka yi wa hukuncin da kashe wani mai suna Rilwanu Ilyasu tun a shekara ta 2016 da ta gabata
  • Mai shari’a ya ce hujjojin da lauyar gwamnati Safiya Yalwati ta gabatar sun tabbatar da laifin, kuma hukuncin ya tabbatar da adalci a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kotu babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutane hudu a jihar kan zargin kisan kai.

Wannan hukunci ya biyo bayan shafe shekaru da aka yi ana shari'a kan zarginsu da hallaka wani mai suna Rilwanu Ilyasu.

Za a rataye mutane 4 a Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An fadi sunayen wadanda ake tuhuma

Kara karanta wannan

Tinubu: Fasto ya tura sako ga Trump kan kashe kashe da ake a Najeriya

Rahoton The Sun ya tabbatar da cewa kisan Rilwanu ya faru ne a shekara ta 2016 bayan an kawo masa farmaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka yanke musu hukuncin sun hada da Abubakar Sadiq da ake kira Alhaji Sallari, Abdulmajid Jibrin, Nasiru Sani, da Yusuf Sani, wadanda duka aka same su da laifin hada baki da kisan kai.

An gurfanar da su bisa dokar laifuffuka sashe na 97 da 221(b), wanda ya haramta aikata irin wannan mummunan laifi.

Rahotanni sun nuna cewa, a ranar 13 ga Afrilu, 2016, wadanda aka yanke musu hukunci sun kutsa gidan mamacin da makamai, ciki har da gatari, suka kai masa hari.

An yankewa mutane 4 hukuncin kisa a Kano
Kakakin yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Musabbabin kai hari kan Rikwanu a Kano

Rahoton kotu ya nuna cewa harin ya samo asali ne saboda zargin cewa mamacin ya sanar da jami’an NDLEA har aka kama daya daga cikinsu tare da kwace masa kwayoyi da kudi N27,000.

Wannan hari ya bar Rilwanu da mummunan rauni wanda daga bisani ya mutu lamarin da ya tayar da hankula jama'a a yankin.

Lauyar gwamnati, Barrista Safiya Yalwati, ta gabatar da shaidu takwas da kuma muhimman kayayyakin hujja ciki har da makamin da aka yi kisan da shi.

Kara karanta wannan

DSS ta tafi kotu da wanda ya nemi a yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Abin da wadanda ake tuhuma suka ce

Bayan nazarin hujjojin, alkalin kotun ya tabbatar da cewa wadanda ake tuhuma sun aikata laifin, don haka ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayan yanke hukuncin, kwamishinan shari’a na Kano, Abdulkarim Maude Kabir, ya yabawa wannan hukunci da aka yanke, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Maude ya fadi haka ne ta bakin mai taimaka masa, Abubakar Tijjani Ibrahim, inda ya ce wannan hukunci na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da adalci da bin doka a jihar.

Za a rataye mutane 3 a Kwara

Mun ba ku labarin cewa wata kotu da ke Ilorin ta sallami mata biyu da ake tuhuma da mallakar bindiga da taimaka wa masu garkuwa da mutane.

Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun kasa kawo hujjojin da ke tabbatar da laifin da ake zargin matan da shi.

Amma kotun ta kuma yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu matasa uku da aka kama da laifin fashi da makami.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.