Malami Ya Fahimci Muhimmin Abu game da Matashin Sojan da Ya Yi Gaba da Gaba da Wike

Malami Ya Fahimci Muhimmin Abu game da Matashin Sojan da Ya Yi Gaba da Gaba da Wike

  • Wani limamin cocin Katolika, Rebaran Fr. Oluoma, ya shiga layin masu tsokaci kan abin da ya faru tsakanin Nyesom Wike da wani sojan ruwa
  • Faston ya bayyana wuraren da matashin sojan ya yi daidai, tare da yabawa yadda ya nuna haƙuri da nutsuwa a lokacin lamarin
  • Sai dai ya jaddada cewa ya dace a ba Ministan Babban Birnin Tarayya goyon baya wajen kwato filaye da aka ba da su ba bisa ka’ida ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani limamin cocin Katolika a Najeriya ya bi sahun masu tofa albarkacin bakinsu kan sa-in-sar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da jami’in sojin ruwa, A.M. Yerima.

Limamin cocin mai suna, Rabaran Fada Oluoma, ya bayyana abin da ya fahimta musamman game da matashin soja, Laftanal Yerima a lokacin da yake musayar yawu da Wike.

Kara karanta wannan

'Ya yi laifi': Asari Dokubo ya fadi matakin da ya kamaci soja bayan rigima da Wike

Fada Oluoma.
Hoton limamin cocin Katolika, Fada Oluoma yna wa'azi ga mabiyansa Hoto: Fada Oluoma
Source: Facebook

Oluoma ya fadi ra'ayinsa game da abin da ya faru ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin cocin ya ce matashin sojan ya nuna haƙuri da natsuwa sosai wajen yadda ya tunkari Wike, duk da zafi da maganganu masu daci da ministan ya rika jifarsa da su.

Laftanal Yerima da wasu sojojin ruwa da yake jagoranta sun hana Wike shiga wani fili da aka ce mallakin tsohon Shugaban Hafsoshin Sojin Ruwa ne.

Abin da malamin coci ya fahimta da Yerima

Da yake bayyana abin da ya fahimta, Fr. Oluoma ya yaba da yadda Yerima ya kasance cikin natsuwa yayin da lamarin ke ƙara ɗumi.

“Ina jinjinawa wannan matashin soja saboda yadda ya iya kwantar da hankali duk da tsokana da kokarin tunzurawa da ya fuskanta.
"Ya cancanci a yaba masa saboda ya kauce wa yin abin da bai dace ba a cikin yanayi mai zafi. Ba abin da ya fi kyau kamar ganin soja mai hali na kirki, wanda ya iya sarrafa kansa.”

Kara karanta wannan

Hadimin Kashim Shettima ya fadi 'mai gaskiya' tsakanin Wike da matashin soja, A.M Yerima

- Fada Oluoma.

Fasto ya ja hankalin Minista Wike

Limamin cocin ya ƙara da cewa kamata ya yi tun farko Wike ya kira wadanda suka turke sojan a wurin ko ya tafi ya dawo wani lokaci domin warware matsalar cikin lumana, maimakon ta kai ga sa-in-sa.

“Sojan yana kan aikinsa ne, kuma yana bin umarnin manyansa. Ya tsaya a kan gaskiyarsa duk da matsin lamba daga Minista.
"A wannan lokaci, ya kamata ace Ministan ya kira manyansa ko ya tafi, daga baya ya dawo, tada hayaniya har da kiran soja ‘wawa’ ba abu ne mai kyau ba," in ji shi.

Oluoma ya bukaci a bar Wike ya yi aikinsa

Sai dai limamin cocin ya kuma bayyana cewa duk da haka, ya kamata a ba Wike goyon baya wajen kwato filayen da aka mallaka ba bisa ka’ida ba.

“Na ga wasu suna murna saboda an taka wa Wike Wike burki, wannan abin dariya ne. Ko baka son mutum, idan yana aikin doka ne, to ya kamata a goya mi shi baya.

Kara karanta wannan

A.M Yerima da Wike: Jerin mutane 4 da ke da karfin ikon bai wa soja umarni a Najeriya

"Matsayin Ministan Abuja yana da ikon kwato filaye da aka mallama ta haramtacciyar hanya, amma abin da muke so shi ne a yi hakan cikin tsari da ladabi.”
Am Yerima.
Hoton sojan Najeriya da ya yi takaddama da ministan Abuja, Laftanal A. M Yerima Hoto: A. M Yerima
Source: Twitter

Atiku ya ba Yerima kyautar mota?

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya fito ya karyata labarin da ke cewa ta bai wa Laftanal Ahmad Yerim, matashin sojan ruwan da ya yi takaddama da Wike kyautar mota.

Labarin ya fara yawo ne bayan takaddamar da ta faru tsakanin Yerima da ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike a ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban kasar bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262