Tirkashi: An Kama Ma'aikatan Majalisar Najeriya da Laifin Damfarar Naira Miliyan 4.8

Tirkashi: An Kama Ma'aikatan Majalisar Najeriya da Laifin Damfarar Naira Miliyan 4.8

  • ICPC ta samu nasarar gurfanar da jami’an Majalisar Dokoki Mustapha Mohammed da Tijjani Adam Goni kan zargin damfarar neman aiki
  • Sun damfari mutane biyu N4.8m da ikirarin neman musu aiki a CBN da FIRS kafin su karyata
  • Kotu ta umurce su da mayar da kudin da suka karɓa da kuma biyan tara na N100,000 kowannensu bayan amincewa da laifi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta samu hukunci bayan gurfanar da ma'aikatan majalisar tarayya biyu, Mustapha Mohammed da Tijjani Adam Goni.

ICPC ta gurfanar da Murstapha da Tijjani ne bisa zargin damfarar wasu mutane da sunan neman musu aiki a Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Haraji ta FIRS.

An kama ma'aikatan majalisar tarayya da laifin damfarar mutane N4.8m.
Hoton ginin majalisar tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @nassnigeria
Source: Twitter

Ma'aikatan majalisar tarayya sun yin damfara

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya bai wa A.M Yerima kariya bayan takaddama da Wike

A cewar rahoton da ICPC ta wallafa a shafinta, wadanda aka gurfanar sun karɓi N4.8m daga Saifudeen Yakub da Aminu Abubakar, da alƙawarin za su samu takardar aiki daga CBN da FIRS.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken ICPC ya nuna cewa a ranar 27 ga Mayu, 2021, wani mutum mai suna Mustapha Muhammed (wanda ya ake nema yanzu) ya ce yana da alaƙa da jami’an majalisa kuma zai iya samawa mutane aiki a CBN ga duk wanda zai biya shi N4m.

An wadanda suka shigar da korafin sun tura masa N3m ta asusun bankin Zenith mai lamba 1000765449, mallakar Mustapha Mohammed.

Daga bisani, a ranar 27 ga Afrilu, 2021, suka sake karɓar N300,000 daga kowane mutum don “binciken lafiya,” ta asusun Access Bank mai lamba 0090719034.

ICPC ta gurfanar da su a gaban kotu

Bayan bincike, ICPC ta gurfanar da su a gaban Mai Shari’a B.M. Bassi na Babbar Kotun Abuja.

Lauyar hukumar, Fatima Abdullahi Bardi, ta bayyana cewa ana tuhumar wadanda ake kara da laifuffuka biyar, ciki har da damfara da ƙirƙirar takardar aiki ta bogi daga CBN da FIRS.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa yunkurin sace jami'ansu da limamin addini a Abuja

A cewar tuhumar, takardun ƙarya da suka fitar sun ƙunshi wasiƙar aiki da ke ɗauke da takarda daga CBN da kuma wasiƙar bogi daga FIRS da aka yi wa wani Mustapha Muhammad.

Hukumar ICPC ce ta gurfanar da ma'aikatan majalisar tarayya a babbar kotun tarayya Abuja.
Ofishin hukumar yaki da ci hanci da rashawa ta ICPC. Hoto: @icpcnigeria
Source: Original

Sun amince da laifi, kotu ta yanke musu hukunci

Bayan da aka fara shari’a, waɗanda ake tuhuma sun amince da laifinsu bisa yarjejeniyar neman afuwa bisa Sashe na 270 na ACJA 2015, inda suka yarda da cewa za su mayar da dukkan N4.8m da suka karɓa.

A ranar 29 ga Oktoba, 2025, kotu ta same su da laifin bada bayanan ƙarya bisa Sashe na 25 na Dokar ICPC ta 2000, sannan ta umurce su da biyan tara na N100,000 kowannensu bayan mayar da kuɗin da suka karɓa.

Shugaban ICPC ya samo mafita ga Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya yi magana kan matsalar cin hanci.

A cewarsa, cin hanci ya daɗe yana addabar kasar nan, kuma ya raunana tattalin arziki, kara rashin tsaro da kuma sa jama’a kin yarda hukumomin gwamnati.

Musa Adamu Aliyu ya yaba wa gwamnatin jihar Borno bisa fifita gyaran tsarin shari’a, yana mai cewa irin wannan kokari zai taka muhimmiyar rawa a yaki da cin hanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com