Dan Majalisar Tarayya daga Kaduna Ya Gaji da Rikicin PDP, Ya Sauya Sheka zuwa APC

Dan Majalisar Tarayya daga Kaduna Ya Gaji da Rikicin PDP, Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Hon. Daniel Amos, mamba mai wakiltar Jema'a da Sanga daga jihar Kaduna a Majalisar Wakilai ya fice daga PDP zuwa APC
  • Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanta wasikar sauya shekar Amos a zaman yau Laraba a Abuja
  • Hon. Amos ya ce rikicin cikin gida da har yanzu aka gaza warware ne ya kore shi daga babbar jam'iyyar adawa ta kasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya - Jam'iyyar APC ta samu karin mambobi a Majalisar Wakilan Tarayya, lamarin da ya kara mata karfi yayin da ake shirin zaben 2027.

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da Harkokin Gida, Hon Daniel Amos, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki Najeriya.

Amos da shugaban Majalisar Wakilai.
Hoton Hon. Danile Amos da shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas Hoto: Hon. Daniel Amos
Source: Facebook

The Nation ta tattaro cewa Hon. Amos, mai wakiltar mazabar Jema’a/Sanga ta jihar Kaduna, ya fara sanar da sauya shekar ta sa ne a wani taro da aka gudanar a filin wasa na Kafanchan.

Kara karanta wannan

Gwamna Caleb ya kammala shirin komawa APC, an ji abin da ya tattauna da Tinubu

Dan Majalisa daga Kaduna ya koma APC

Sai dai a yau Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025, dan majalisar ya tabbatar da matakin da ya dauka na komawa APC a zauren Majalisar Wakilai da ke Abuja.

A cikin wata wasika da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya karanta a zauren majalisar, Amos ya bayyana cewa rikicin cikin gida ne ya koro shi daga PDP.

Ya ce rikice-rikicen da PDP ke fama da su a matakin kasa, wadanda har yau ta gaza warware wa, sun rage mata karfin gudanar da ayyukanta da kokarin kare muradan jama'a.

Dan majalisar ya ce hakan ya tilasta masa neman wani dandalin siyasa mai zaman lafiya, wanda zai ba shi damar gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Abin da ya kori Hon. Amos daga PDP

Ya bayyana cewa wannan mataki ya na da matukar wahala a gare shi, musamman ganin cewa PDP ce ta ba shi damar zama wakili a Majalisa bayan shekaru na sadaukarwa da hidima ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Hon. Amos ya nuna nadama kan yadda PDP ta lalace, yana mai cewa jam'iyyar ta bar kanta cikin rikice-rikice, wadanda suka sa jama'a suka fara sauka daga layinta.

Majalisar Wakilai.
Hoton zauren Majalisar Wakilan Tarayya da ke Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Ya kara da cewa bayan tuntubar jama’arsa, ya yanke shawarar hada kansa da manufofin gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dan Majalisar ya ce ya yi haka ne domin kawo karin ci gaba ga mazabarsa, tare da goyon bayan kokarin Gwamna Uba Sani na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a jihar Kaduna.

An yi hayaniya a Majalisar Wakilai

A wani rahoton, kun ji cewa rikiici da hayaniya sun barke a zaman Majalisar Wakilai ta tarayya a ranar Talata kan zargin sayar da kayan gwamnati ba bisa ka'ida ba a Legas.

Yayin da hayaniya ta yi kamari, Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda ke jagorantar zaman, ya shiga tsakani don kwantar da hankalin abokan aikinsa.

Duk da kokarin Benjamin Kalu, yan majalisar sun ci gaba da musayar yawu, lamarin da ya tilasta masa ba da umarnin komawa zaman sirri don warware matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262