Hafsan Sojan Kasa Janar Shaaibu Ya Gana da Tinubu, Ya ba Shi Bayanan Tsaro

Hafsan Sojan Kasa Janar Shaaibu Ya Gana da Tinubu, Ya ba Shi Bayanan Tsaro

  • Shugaba Bola Tinubu ya karɓi rahoton tsaro daga Babban Hafsan Sojan Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, kan halin da ake ciki a Arewa maso Gabas
  • Wannan shi ne karo na farko da Shugaban ƙasa ke gana wa ta aiki da sabon hafsan sojoji tun bayan nadinsa da sauran takwarorinsa
  • Janar Shaibu ya ce rahoton nasa ya ta’allaka ne kan cigaban da aka samu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma yanayin tsaro a faɗin ƙasar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi cikakken rahoton tsaro daga Babban Hafsan Sojan Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.

Rahoton ya kunshi yadda ake gudanar da yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da halin da kasa ke ciki ta fuskar tsaro.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

Janar Shaaibu ya gana da Tinubu
Hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Shaaibu, Bola Ahmed Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa wannan shi ne ganawar farko ta aiki tsakanin Tinubu da sabon hafsan sojojin tun bayan nadinsa da kuma sanya masa alamar mukami a makonnin da suka gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hafsan soja ya gana da Tinubu

Arise News ta wallafa cewa Laftanal janar Shaibu ya ce ya ziyarci yankin domin gane wa idanunsa yadda ake tafiyar da ayyukan soji a Arewa maso Gabas.

Haka kuma ya tantance irin nasarorin da aka samu a fafutukar kawar da ‘yan ta’adda da sauran barazanar tsaro a shiyyar.

Ya ce:

“Na zo ne in bayyana wa Shugaban Ƙasa sakamakon ziyarata zuwa Arewa maso Gabas da kuma sauran yankuna na ƙasa. A halin yanzu, muna ganin kyakkyawan cigaba.”

Da aka tambaye shi abin da ‘yan Najeriya za su iya tsammani bayan wannan ziyara, Janar Shaibu ya ce a sa rai da samun ingantaccen tsaro a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa

Tinubu ya gargadi hafsoshin tsaro

Janar Shaibu na daga cikin sababbin shugabannin rundunonin tsaro da Shugaba Tinubu ya nada a baya-bayan nan.

Sauran sun haɗa da Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro da Vice Admiral Abbas a matsayin Babban Hafsan Rundunar Ruwa.

Laftanal Janar Waidi Shaaibu ya bai wa Tinubu bayanan tsaro
Hafsan Sojan Kasa Laftanal Janar Waidi Shaaibu Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Shugaba Bola Tinubu ya kuma nada Air Marshal Kelvin Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama.

A lokacin da Shugaban ƙasa ya ke musu jawabi bayan nadin nasu, ya ja hankalinsu da su gudanar da aikinsu da ƙwazo da kishin ƙasa.

Ya umarce su da tabbatar da cewa kasar nan ta samu tsaro domin a samu wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al'umma.

An shawarci Tinubu kan rashin tsaro

A baya, kun ji cewa dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo a yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus.

Ya bayyana haka ne saboda a cewarsa, rashin tsaro ya yi ƙamari gaske, kuma dole Shugaban ya dauki matakai da suka dace wajen ceto rayukan talakawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

Adebayo ya ce shugaban ƙasa na da zaɓi biyu, ko ya yi amfani da harsashi ya kashe ‘yan ta’adda, ko kuma ya yi amfani da alƙalami ya yi murabus daga ofis.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng