Tura Ta Kai Bango: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bukaci Tinubu Ya Yi Murabus
- Adewole Adebayo ya ce ya zama dole ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da karfin bindiga wajen kashe ‘yan ta’adda
- Idan ya gaza kawar da 'yan ta'adda, to dan takarar shugaban kasar ya ce dole ne Shugaba Tinubu ya yi murabus
- Adebayo ya gargadi ‘yan siyasa da su guji amfani da kalaman Donald Trump kan Kiristoci wajen tayar da rikicin addini a kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus.
Prince Adewole Adebayo ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya ɗaukar matakin gaggawa wajen kawo karshen matsalar tsaro a ƙasar ba.

Source: Twitter
An bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus
Jaridar Vanguard ta rahoto Prince Adebayo yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ko dai Shugaba Tinubu ya yi amfani da harsashi ya kashe ‘yan ta’adda, ko kuma ya yi amfani da alƙalaminsa ya yi murabus kawai.”
Adebayo ya bayyana haka ne a taron garambawul kan harkokin zabe na kasa da aka gudanar a Abuja a ranar Talata wanda kungiyoyin NCFront da LCSF suka shirya.i
Adebayo ya yi wannan jawabi ne a yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan maganganun Shugaban Amurka Donald Trump.
Idan ba a manta ba, Shugaba Trump ya zargi ƙungiyoyin da ke yaki da sunan Musulunci da kai hare-hare kan Kiristoci a Najeriya.
An zargi shugabanni kan tsawaitar matsalar tsaro
Dan takarar SDP ya gargadi ‘yan siyasa da su guji amfani da wannan batu wajen ƙara raba kan ‘yan Najeriya ta fuskar addini.
“Sojojin Najeriya, yadda na san su, za su iya kare duk yankin Yammacin Afirka idan aka bar su su yi aikinsu. Amma idan gwamnati ta hana su, za su kasa kare 'yan ta'addan cikin gida."
- Prince Adewole Adebayo.
Ya kuma zargi shugabanni na baya da na yanzu da cin moriyar matsalar tsaro don amfanin kansu, yana mai cewa jagoranci mai ƙarfi da gaskiya ne kawai zai kawo ƙarshen wannan matsala cikin gaggawa.

Source: Facebook
“Trump ba zai iya warware matsalar Najeriya ba”
Adebayo ya ce ko da yake yana yi wa Trump godiya kan yadda ya nuna damuwa game da Najeriya, bai kamata a juya hakan zuwa rikicin addini ba.
“Ina godiya ga Mista Trump saboda nuna damuwarsa kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, amma bai kamata mu mayar da kalamansa zuwa rikicin Kirista da Musulmi ba.
"Wanda ke son taimaka wa Najeriya, ya taimaka wa kowa ba tare da wariya ba. Matsalarmu za ta warware ne idan shugabannin cikin gida suka yi aikinsu."
- Prince Adewole Adebayo.
2027: Amaechi ya ce za a iya doke Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya nemi jam’iyyun adawa su tashi tsaye su shirya kafin zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya ce za a iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaben mai zuwa, amma dole sai idan ‘yan ƙasa sun fito kwansu da kwarkwata.
Tsohon gwamnan Amaechi ya ce NLC, ASUU ko NANS kadai ba za su iya ba, dole sai jama'a sun dauki nauyin kare dimokuradiyya da kansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


