"Za a Iya Kifar da Shi": Amaechi Ya Hango Hanyar Kayar da Tinubu a Zaben 2027

"Za a Iya Kifar da Shi": Amaechi Ya Hango Hanyar Kayar da Tinubu a Zaben 2027

  • Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasar Najeriya na shekarar 2027 da ake tunkara
  • Rotimi Amaechi ya bukaci 'yan Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu don ganin cewa sun kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben
  • Tsohon ministan ya nuna cewa kayar da shugaban kasan ba wani abu ba ne wanda ba zai taba yiwuwa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya kan zaben 2027.

Amaechi ya bukaci 'yan Najeriya su shirya kada kuri’a sosai a 2027 domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai samu wa’adi na biyu ba.

Amaechi ya ce za a iya kifar da Tinubu a 2027
Shugaban kasa Bola Tinubu da Rotimi Amaechi Hoto: @OfficialABAT, @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru biyar na jaridar First Daily da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Abubuwa da ya kamata ku sani game da Gwamna Soludo da ya lashe zaben Anambra

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Amaechi ya ce kan kifar da Tinubu?

Amaechi, wanda a watan Agusta ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce rashin nasarar da Tinubu ya yi a jihar Legas a 2023 ta nuna cewa za a iya kayar da shi.

A jawabin da ya yi, Amaechi ya gargaɗi ‘yan Najeriya kan sakaci da rashin fitowa wajen kada kuri’a, yana mai cewa hakan yana ba wa maguɗin zaɓe damar yin tasiri, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

“Mataki na farko wajen gyaran tsarin zaɓe ba daga gwamnati yake ba, daga mutane yake. Mutane su ne matsalar."
"Idan har mutane suna cewa ‘an riga an rubuta sakamako,’ hakan ke jawo musu kasala. Wannan kasala ce za ta sa Tinubu ya koma Villa a karo na biyu.”
“Ku gaya wa mutane cewa iko yana hannunsu. Ku fito. Idan Tinubu yana da ikon da ba za a iya kayar da shi ba, ta yaya aka kayar da shi a Legas?"

Kara karanta wannan

Kashim Shettima na da hannu a kafa Boko Haram? Ali Modu Sherrif ya fadi gaskiya

"Ana iya maimaita hakan, amma dole ne a fara da fahimtar cewa mutumin nan za a iya kayar da shi. Matsalar ita ce adawa.”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya yabo batun gyaran tsarin zabe

Amaechi ya ce ba a taba samun wata gwamnati mai ci da ta yi gyaran tsarin zaɓe mai inganci ba, saboda masu ruwa da tsaki a cikin siyasa na kawo cikas a kokarin canji don kare muradunsu.

Amaechi ya soki 'yan adawa a Najeriya
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter
“Matsalar zaɓe a Najeriya ita ce babu wata gwamnati mai ci da za ta iya aiwatar da sahihin gyaran tsarin zaɓe. Mun gwada a baya, kuma mun gaza."
Ya kuma zargi jam’iyyun adawa da rashin tsari da hadin kai, yana mai cewa hakan yana raunana karfinsu na kalubalantar jam’iyya mai mulki.
“Na gaya wa jam’iyyun adawa cewa su ne matsalar. Ba sa tattauna yadda za a ceci Najeriya. Babu wanda yake cewa, ‘eh, abubuwa sun tabarbare, ta yaya za mu canza shugabanci?’”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya ba gwamnati shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya samo mafita ga gwamnati kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Rotimi Amaechi ya ce yaki da rashin tsaro ba zai haifar da sakamako mai kyau ba muddin gwamnati ba ta magance matsalar yunwa a tsakanin ‘yan kasa ba.

Tsohon ministan ya ce dogaro kawai da karfin soja ko ‘yan sanda wajen yaki da rashin tsaro ba tare da magance talauci da yunwa ba, na kara haifar da rikice-rikice da rashin kwanciyar hankali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng