Boko Haram da ISWAP Sun Yi Azababben Artabu, Sama da Mutum 200 Sun Bakunci Lahira
- Mayakan Boko Haram da na ISWAP sun yi azababben gumurzu a tsakaninsu a yankin Tafkin Chadi ranar Lahadi da ta gabata
- Majiyoyi daga yankin sun bayyana wannan fada da ya auku tsakanin kungiyoyin yan ta'addan a matsayin mafi muni tun bayan rabuwarsu
- Akalla yan ta'adda 200 ne aka ruwaito cewa sun mutu a musayar wuta, lamarin da jami'an tsaro suka ce labari ne mai dadi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Kungiyoyin 'yan ta'adda, Boko Haram da ISWAP da ke kai hare-hare a Arewa maso Gabashin Najeriya sun yi azababben artabu a yankin Tafkin Chadi.
Majiyoyi daga jami'an leken asiri, 'yan sa-kai da tubabbun yan ta'adda sun nuna cewa rigima tsakanin kungiyoyin ta kara kamari a baya-bayan nan.

Source: Twitter
An kashe yan ta'adda sama da 200
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa akalla yan ta'adda 200 suka mutu a musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram da ISWAP a yankin Tafkin Chadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa rikici ya barke tsakanin Boko Haram da kungiyar ISWAP a yankin Dogon Chiku da ke gefen Tafkin Chadi a ranar Lahadi.
Majiyoyi sun ce mayakan kungiyoyin sun yi ta fafatawa mai tsanani kan mallakar yankin da kuma sabanin ra’ayoyi tsakanin bangarorin biyu.
Babakura Kolo, wani dan kungiyar sa-kai da ke taimaka wa rundunar sojin Najeriya, ya ce:
“Daga bayanan da muka samu, sama da ‘yan ta’addan ISWAP 200 ne suka mutu a wannan gumurzu."
Boko Haram da ISWAP sun rasa mayaka
Wani tsohon dan Boko Haram da ya tuba, amma yana bibiyar ayyukan kungiyoyin, ya tabbatar da cewa “kimanin mayakan ISWAP 200 ne suka mutu a artabun tare da kwace makamansu."
A cewarsa, Boko Haram ta rasa mayaka hudu a fadan, inda ya bayyana wannan rikici da “fadan da ya fi tsanani tsakanin kungiyoyin tun bayan rabuwarsu.”
Saddiku, wanda ke zaune a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ya ce:
“Wannan na iya zama rikicin da ya fi muni tun daga lokacin da suka fara kai wa juna hare-hare."
Jami'an tsaro sun ji dadin abin da ya faru
Wani jami’in leken asiri a Najeriya da ke aiki a yankin ya tabbatar da cewa hukumomi na bibiyar sakamakon rikicin, yana mai hasashen cewa mutane sama da 150 ne suka mutu, in ji rahoton Guardian.
"Mun samu labarin wannan fada, kuma a gare mu wannan labari ne mai dadi,” in ji jami’in leken asirin.

Source: Twitter
Tun bayan rabuwar Boko Haram da ISWAP a 2016 saboda sabanin ra’ayoyi, kungiyoyin biyu su na fada a tsakaninsu kan mallakar yankuna, musamman a yankunan da ke kewaye da Tafkin Chadi.
Sojoji sun ceto mutane 86 A Borno
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su a tsakanin yankin Buratai zuwa Kamuya da ke jihar Borno.
Dakarun sojojin sun kuma kai samame sansanin mayakan Boko Haram da ISWAP da ke yankin, kuma sun yi nasarar ragargaza shi gaba daya.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
A yayin wannan hari, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin tserewa da mutanen da suka sace a cikin motoci guda biyu amma sojoji suka ci karfinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

