Jerin Kungiyoyin Duniya da Suka Karyata Trump kan Zargin da Ya Yi wa Najeriya
Manyan kungiyoyin duniya da suka hada da ECOWAS sun yi martani kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump ta kawo farmaki Najeriya.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kawo farmaki Najeriya domin kashe 'yan ta'adda a Arewacin kasar.
Donald Trump ya ce zai kawo farmakin ne bayan zargin da ya ce ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a kasar ba tare da gabatar da gamsassun dalilai ba.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari tare da tattaro bayanan da manyan kungiyoyin duniya suka yi bayan barazanar Trump ga Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. ECOWAS ta karyata ikirarin Trump
Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce ikirarin cewa ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya na nufin kara dagula harkokin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan
"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya
A cikin wata sanarwa da ta fitar, the Cable ta rahoto cewa kungiyar ta bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci masu salo daban-daban suna kashe Musulmi da Kirista.

Source: Facebook
“Binciken kungiyoyi masu zaman kansu a tsawon shekaru ya tabbatar da cewa tashin hankalin da ya shafi ta’addanci ba ya bambance tsakanin jinsi, addini, kabila ko shekaru,”
Inji sanarwar
Kungiyar ta kara da cewa:
“ECOWAS na kira ga majalisar dinkin duniya da dukkan abokan hulɗa da su tallafa wa kasashe wajen yaki da wadannan kungiyoyi,
"Mun nuna kin amincewa da duk wani ikirari da ke cewa kungiyoyin ta’addanci na kai hari ga rukuni guda, ko cewa ana kisan kiyashi na wani addini a yankin,
“ECOWAS ta ƙi amincewa da wannan ikirari na karya mai hatsari da nufin kara dagula tsaro da kuma raunana hadin kai tsakanin al’umma a yankin,”
Kungiyar ta kuma bukaci al’ummar duniya da su tsaya tare da kasashen yankin wajen yakar ta’addanci.
2. AU ta ki yarda da maganar Trump
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta ƙi amincewa da zargin da Amurka ta yi cewa ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da hukumar zartaswar kungiyar (AUC) ta fitar, ta bayyana rashin amincewarta da ikirarin da ke zargin Najeriya da sakaci da lamarin tsaro.
Legit ta rahoto cewa kungiyar ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro masu rikitarwa da ke shafar ‘yan ƙasa na dukkan addinai.

Source: Facebook
Ta ce kasar na fama da matsalolin ƙungiyoyin tsageru masu tsattsauran ra’ayi, ‘yan fashi, rikicin kabilanci, da kuma rikice-rikicen da suka shafi albarkatun ƙasa.
Premium Times ta ce AU ta jaddada cewa Najeriya na da cikakken ‘yancin gudanar da harkokinta na cikin gida bisa tsarin kundin mulkinta da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa.
“Dole duk wata hulɗar waje ta girmama ikon mallaka na Najeriya, iyakokinta, da hadin kanta,”
Inji sanarwar
3. EU ta kare Najeriya kan zargin Trump
Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta bayyana cewa ba addini ba ne sanadin tashin hankali a Najeriya, tare da jaddada goyon bayanta ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kare al’ummar ƙasar.
EU ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafawa zaman lafiya, ‘yancin yin addini, da kare dukkan al’umma a Najeriya, bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa ƙasar.

Source: Facebook
Business Day ta wallafa cewa da yake magana game da matsayar gwamnatin Amurka, mai magana da yawun EU kan harkokin wajen ƙungiyar, Anouar El Anouni ya ce:
“Tarayyar Turai tana mika ta’aziyyarta ga dukkan al’ummomi da iyalai da suka rasa ‘yan uwa sakamakon tashin hankali, ciki har da hare-haren baya-bayan nan da suka faru a yankin Kudu da Arewa maso Gabas na Najeriya.
“Muna sake tabbatar da aniyarmu ga ‘yancin yin addini da kuma kare dukkan al’umma, musamman marasa rinjaye,”
Trump: Momodu ya ba Tinubu shawari
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon dan siyasa kuma dan jarida, Dele Momodu ya ce ya kamata Bola Tinubu ya dauki mataki game da barazanar Donald Trump.
Momodu ya bukaci shugaban kasar ya hada kan manyan kasa su tattauna da Donald Trump domin warware sabanin.
Ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta kalli matsalar a matsayin abin da ya shafi kasa ba ta siyasa ba kamar yadda wasu suka fara jingina shi ga 'yan adawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

