Bayan Gargadin Birtaniya, Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Sakamakon Yaki da Ta'addanci na 2025

Bayan Gargadin Birtaniya, Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Sakamakon Yaki da Ta'addanci na 2025

  • Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu nasarar shawo kan matsalar tsaro da ake fama da shi a kusan dukkanin sassan kasar
  • Wannan na zuwa ne bayan gargadin da Birtaniya ta bai wa 'yan ƙasarta da su guji tafiya wasu yankuna saboda hare-haren ta’addanci
  • Haka kuma Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi kakkausan kalamai a kan tsaron Najeriya, musamman ga kiristoci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatin kasar nan ta bayyana cewa an samu gagarumar nasara wajen rage matsalar tsaro da ta dabaibaye wasu sassan ƙasar tsawon shekaru.

Ta ce sababbin alkaluma da ta tattara daga hukumomin tsaro a shekarar 2025 sun nuna cewa an samu saukin hare-hare da satar mutane.

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu raguwar matsalar tsaro
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa gwamnatin ta ce an samu raguwar ta'addanci da fiye da kashi 80 cikin dari idan aka kwatanta da shekarun baya.

Kara karanta wannan

Abuja: Wike ya taso masu kadarori a gaba, ya ba su kwanakin biyan tarar N5m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati: An samu saukin ta'addanci a Najeriya

Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan jama'a ta kasa ta tabbatar da raguwar matsalolin tsaron a sakon da ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

A cikin wata sanarwa da ofishin Majalisar Tsaron Ƙasa ya fitar, an bayyana cewa an samu wannan nasara ne saboda karin hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro.

Sanarwar ta ce an samu hadin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda, da hukumar DSS inda suka taimaka wajen karya lagon 'yan ta'adda yankunan da ke fama da rikice-rikice.

Wata majiyar gwamnati ta shaida cewa an samu ƙarin kwanciyar hankali a yankunan Borno, Zamfara, da Katsina, inda hare-haren ‘yan bindiga da na ta’addanci suka ragu sosai.

Rahoton Najeriya ya yi martani ga Birtaniya

Rahoton da gwamnatin Najerita ta fitar na zuwa a lokacin da Birtaniya ta fitar da sabon gargadi ga ‘yan ƙasarta, tana shawartar su da su guji tafiya wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware N400bn domin wasu manyan ayyuka a sassan Najeriya

Gwamnati ta ce an samu raguwar matsalolin tsaro musamman a yankunan Arewa
Hoton Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rahoton hukumar tsaron Birtaniya ya jero jihohi kamar Borno, Yobe, Katsina, Zamfara, Adamawa, da Gombe, tare da wasu jihohin kudu.

Ta shaidawa 'yan kasarta cewa akwai yiwuwar faruwar hare-hare, satar mutane ko farmaki kan matafiya a yankunan da ta ayyana.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce an samu 'yar matsala, domin sababbin alkaluma sun nuna raguwar ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Rashin tsaro ya jawo zanga-zanga

A wani labarin, mun wallafa cewa mazauna Isanlu sun fito zanga-zanga lumana a ƙauyen Ilafin‐Isanlu sakamakon wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai jihar Kogi a daren Asabar.

A yayin harin, an kama tsohuwa Elizabeth Olorunshola, amma daga baya sai suka kashe tsohuwar bayan ta gaji kuma ba za ta iya ci gaba da tafiya zuwa maboyarsu a daji ba.

Bayan gano gawar tsohuwar a daji, mazauna yankin sun shiga tashin hankali, kuma suka fara zanga-zanga, yayin da wasu suka fara barin yankin domin tsoron sake fuskantar harin 'yan ta'adda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng