Kogi: Jama'a Sun Barke da Zanga Zanga bayan 'Yan Bindiga Sun Jefa Gawar tsohuwa a Daji

Kogi: Jama'a Sun Barke da Zanga Zanga bayan 'Yan Bindiga Sun Jefa Gawar tsohuwa a Daji

  • Mazauna Isanlu sun tsunduma zanga-zanga bayan wani harin ‘yan bindiga da ya yi sanadiyyar mutuwar wata tsohuwa
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga da suka farmaki yankin sun kashe wata mata mai suna Elizabeth Olorunshola
  • Shugabannin yankin da ‘yan siyasa sun yi Allah wadai da harin tare da neman a dauki matakan tsaro domin rage yawan hare-haren

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi – Mazauna yankin Isanlu a ƙaramar hukumar Yagba East, jihar Kogi, sun shiga tashin hankali bayan wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai masu.

A yayin harin, 'yan ta'addan sun harbi wata tsohuwa mai suna Mrs. Elizabeth Olorunshola a unguwar Ilafin-Isanlu, wanda ya yi sanadin rasuwarta.

Jama'a sun yi zanga zanga a Kogi
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ‘yan bindiga da ake zargin barayin daji ne sun kai farmaki a daren Asabar, inda suka yi garkuwa da matar da wani mutum a kan titin Ilafin-Isanlu Road.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mata 9 a Sokoto, sun hallaka wasu

Jama'a sun shiga takaici a Kogi

Rahoton ya ce majiyoyi sun ce maharan sun kashe matar bayan sun lura da cewa ta gaji kuma ba za ta iya ci gaba da tafiya zuwa maboyarsu ba.

An gano gawarta cikin daji da safiyar Lahadi, abin da ya haddasa firgici da zanga-zangar lumana a yankin domin jawo hankalin mahukunta.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna sun fara barin yankin saboda tsoron 'yan ta'addan za su sake kawo masu sababbin hare-hare.

An yi Allah wadai da harin 'yan bindiga

Shugaban ƙungiyar ci gaban Ilafin, Mista Idowu Awe, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne kuma mai ban tausayi.

Jama'a sun fusata bayan harin 'yan bindiga a Kogi
Taswirar jihar Kogi inda aka kai harin 'yan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

A kalamansa:

“Mun rasa ɗaya daga cikin manyan mata masu daraja a unguwarmu. Wannan abin ya girgiza mu sosai. Tuni dattawa da shugabanni suka fara tattaunawa kan yadda za a kara tsaro a yankin."

Shugaban ƙaramar hukumar Yagba East, Hon. (Dr.) Joshua Dare Monday, ya la’anci harin, yana mai cewa abu ne mai tayar da hankali.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

Shugaban ya kara da cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan ta’asa sun fuskanci hukunci.

A bangarensa, dan majalisa mai wakiltar Yagba East-West/Mopamuro a Majalisar Tarayya, Rt. Hon. Leke Abejide, ya bayyana takaicinsa kan garkuwa da kashe matar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP William Aya, bai ce komai a kan kisan da ake yi wa dattijuwar da zanga-zangar ba.

Sojoji sun ceto mutane a Kogi

A baya, mun wallafa cewa rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa dakarunta sun samu gagarumar nasara a wani aikin musamman da suka gudanar, inda suka ceto mutane 21.

Sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Polycarp Okoye, ya fitar ta ce aikin ya gudana ne karkashin shirin Operation Fansan Yamma a ranar 17 ga Oktoba, 2025.

Ya ce wannan farmaki ya zama wani muhimmin mataki na ci gaba da murkushe ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke addabar al’ummar yankin Arewa ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng