Zabe Ya Bar Baya da Kura, an Bindige Kansila yayin Jefa Kuri’a a Anambra
- Wasu ‘yan bindiga sun harbe kansilan jam’iyya mai mulki a jihar Anambra yayin gudanar da zaben gwamnan da aka yi
- Maharan sun zo a mota inda suka harbe kansilan jam'iyyar APGA, Nze Ala Kuru Orji, yayin da yake jefa ƙuri’a a mazabar Ezukaka 1
- Lamarin ya tayar da hankulan mutanen da ke wurin wanda ya faru a karamar hukumar Orumba ta Kudu a ranar Asabar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji a lokacin da yake jefa ƙuri’a a Orumba ta Kudu.
Hakan ya faru ne a ranar Asabar 8 ga watan Nuwambar shekarar 2025 yayin da ake gudanar da zaben gwamna a Anambra.

Source: Facebook
An bindige kansila yayin zabe a Anambra
Lamarin ya faru ne ranar Asabar a mazabar Ezukaka 1 da misalin ƙarfe ɗaya na rana, lokacin da ake tsakiyar zaɓen gwamna, cewar rahoton Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu shaidun gani da ido da suke wurin sun tabbatar da cewa ana tsaka da kada kuri'a ne wasu matasa suka zo suka bude masa wuta.
Wani ganau ya ce:
“Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke rufe da fuska suka bayyana suka harbe mutumin nan, daga nan suka tsere da motarsu ba tare da cutar da wani ba."
Masu jefa ƙuri’a da dama sun shiga fargaba, inda wasu suka bayyana damuwa kan yiwuwar tashin hankali kafin a kammala zaɓen gaba ɗaya.
Wani mazaunin yankin ya ce:
“Abin ya firgita mu. Ba a taɓa samun irin wannan kisa a wannan mazaba ba."

Source: Original
An tabbatar da zuwan jami'an tsaro wurin
Wani mai suna Odemenna ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun iso wurin don gudanar da bincike da kuma neman waɗanda suka hallaka kansilan.
A cewar Chukwudi Chinanso:
“Maharan sun kai harin ne kan kansilan, kuma sun tarar da shi ne lokacin da ya zo jefa ƙuri’a.”
Majiyoyi suka ce lamarin ya jefa mazauna yankin cikin tsoro da damuwa sosai duba da har yanzu ba a gano dalilin kisan ba, Daily Post ta tabbatar.
Wata mata mai suna Joyce Okoro ta ce:
“Wasu matasa ɗauke da makamai sun zo mazabar mu suka harbe kansilan sannan suka tsere.”
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin rikicin siyasa ne ya haddasa kisan, kasancewar Nze Orji ɗaya ne daga shugabannin jam’iyyar APGA a mazabar.
Abin da yan sanda suka fadawa Legit Hausa
Har lokacin tattara wannan rahoto, rundunar yan sanda Anambra ba ta fitar da sanarwa ba game da lamarin da ya faru.
Sai dai kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa bai da labarin abin da ake magana a kai har yanzu.
Jami'ar INEC ta yanke jiki ta fadi ana zabe
Kun ji cewa wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS.
Dubban masu jefa kuri’a a Enugwu-Ukwu sun kasa kada kuri’unsu saboda BVAS ta gaza tantance katin masu zabe.
Hukumar INEC dai ta ce ta dora fiye da 95% na sakamakon zaben gwamnan Anambra a shafinta na IReV da ke intanet.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


