An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

An kashe wani kansilar karamar hukuma a jihar Anambra, Chukwuebuka Ikeji a kan rikicin fili.

Sakamakon hakan, fusatattun matasa a unguwar sun hada kai sun kone gidan Emmanuel Ukandu wanda ake zargi da kashe kansilar.

Har wa yau, matasan sun kuma kona motar bus mallakar Emmanuel Ukandu da ake zargin da ita ya kashe kansilar.

Lamarin ya faru ne a garin Umunna, Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu na jihar ta Anambra.

An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili
Source: UGC

An gano cewa Ukandu wanda suka samu rashin jituwa da mammacin saboda fili ya yi amfani da motarsa ne ya nike shi duk da gargadin da yaron motarsa ya masa kan afkuwar hakan.

DUBA WANNAN: Coronavirus: An jefi jami'an tsaron gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC a jihar, Edwin Okadigbo ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin.

Ya ce an sanar da ofishin NSCDC na Orumba ta Kudu afuwar lamarin a ranar Laraba.

Okadigbo ya ce, "Binciken da muka gudanar kawo yanzu ya nuna cewa wanda ake zargin ya dade yana rikici da mutane kan mallakin wata fili kuma yana jin haushin duk wadanda ba su goyon bayansa.

"Garin haka ne ya kashe mammacin wanda shine kansila mai wakiltan Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu, har yaron motarsa ma ya yi ta faɗa masa cewa idan bai dakatar da motarsa ba zai buge mutumin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel