Kashim Shettima na da Hannu a Kafa Boko Haram? Ali Modu Sherrif Ya Fadi Gaskiya

Kashim Shettima na da Hannu a Kafa Boko Haram? Ali Modu Sherrif Ya Fadi Gaskiya

  • Sanata Ali Modu Sherrif ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya zargi Kashim Shettima da hannu a kafa Boko Haram
  • Tsohon gwamnan jihar Borno ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne kuma an kirkire shi ne domin ba ta masa suna
  • Ya sha sha alwashin cewa ba zai bar wannan abin ya wuce haka nan ba, zai dauki matakin shari'a domin hukunta masu hannu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya karyata rahoton da ke cewa ya zargi Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da kafa Boko Haram.

Wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Ali Modu Sheriff ya fito ya tabbatar da cewa, “Ba ni bane, Shettima ne ya ƙirƙiri Boko Haram.”

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Sanata Ali Modu Sherrif.
Hoton tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif Hoto: Muhammad Ibrahim Umar
Source: Facebook

Da gaske Sherrif ya zargi Kashim Shettima?

Binciken da jaridar The Cable ta gudanar ya nuna cewa karon farko da aka wallafa wannan rahoton shi ne a watan Agustan shekarar 2016.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Modu Sherrif ya bayyana wannan labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta a matsayin labarin “ƙarya, makirci kuma wanda aka kirkira domin hada haɗa fitina.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Sheriff ya ya ce labarin a matsayin “karya tsantsa” da aka kirkria da gangan da nufin ruɗar da jama’a da tayar da rikicin siyasa.

A rahoton Daily Trust, sanarwar ta ce:

“Labarin da ake yadawa ƙarya ce tsantsa wacce ba ta da wani tushe ko kanshin gaskiya a cikinta. An tsara shi ne domin ɓata sunan Sanata Sheriff da haddasa rikici a siyasar ƙasa.”

Ali Modu Sherrif ya fayyace gaskiya

Tsohon gwamnan Borno ya bayyana cewa bai taɓa yin hira ko ya yi magana da ɗan jarida kan wannan batu ba, yana mai cewa an shirya wannan labari ne domin ɓata sunansa.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Wannan rahoto cike yake da yaudara kuma ba shi da kusanci da gaskiya, sannan labarin babban haɗari ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman ganin irin rawar da Sanata Sheriff ya taka wajen samar da zaman lafiya a Borno da ma fadin ƙasar nan.”

Tsohon gwamnan ya roƙi jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da labarin, yana mai bayyana cewa ya umarci lauyoyinsa su gano duk wanda ke da hannu wajen yada ƙaryar.

Kashim Shettima da Ali Modu Sherrif.
Hoton mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Sanata Ali Modu Sherrif Hoto: @OfficialSKSM, Muhammad Ibrahim Umar
Source: Facebook

Wane matakin tsohon gwamnan ya dauka?

A ƙarshe, Sheriff ya jaddada ƙudurinsa na ci gaba da bada gudummuwa wajen inganta tsaro, zaman lafiya da dimokuraɗiyya a Najeriya

Ya kuma tabbatar da cewa ba zai bar yaɗa ƙarya da yaudara irin wannan da ta hada har da kokarin bata sunan mataimakin shugaban kasa, ya wuce ba tare da daukar mataki ba.

Sojoji sun dakile harin Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram/ISWAP a sansaninsu na Kangar, da ke Mallam Fatori a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu

An ruwaito cewa rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda shida, ta kwato bindigogi, alburusai, da jirage marasa matuƙa guda hudu.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na asuba, inda ‘yan ta’addan suka yi amfani da jirage marasa matuka masu ɗauke da makamai wajen kai harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262