Ana cikin Kada Kuri'a, Gwamna Soludo Ya Cika Baki kan Zaben Anambra

Ana cikin Kada Kuri'a, Gwamna Soludo Ya Cika Baki kan Zaben Anambra

  • Farfesa Charles Soludo ya kada kuri'arsa a zaben gwamnan jihar Anambra da ake gudanarwa a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025
  • Gwamnan wanda yana daya daga cikin 'yan takara ya nuna kwarin gwiwar samun nasara kan abokan hamayyarsa da suke fafatawa a zaben
  • Sai dai, Gwamna Soludo ya bayyana cewa sun bankado wani shiri na shirya rashin gaskiya wajen fitar da sakamakon zaben na jihar Anambra

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Anambra - Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Chukwuma Soludo, ya yi magana kan zaben gwamna da ake gudanarwa a jihar.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa jam’iyyarsa za ta yi nasara da babban rinjaye a zaben gwamnan jihar da ke gudana.

Soludo ya hango nasara a zaben gwamnan Anambra
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Twitter

Me Soludo ya ce kan zaben Anambra?

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa Farfesa Soludo, wanda ke fafatawa da wasu ‘yan takara 15, ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Reshe zai juye da mujiya, Gwamna mai ci ya zargi 'yan adawa da sake kudi a zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin da nake so shi ne jama’a su fito su kada kuri’unsu. Mun tabbata cewa za mu yi nasara, kuma nasarar za ta kasance da babban rinjaye."
“Kamar yadda kuka gani, tsarin zaben yana tafiya cikin sauƙi. Mun faɗa tun lokacin yakin neman zaɓe cewa muna da masu adawa, amma ba mu ga wata gagarumar adawa. Amma duk da haka, ba za mu ɗauki ƙuri’un jama’a da wasa ba.”

- Farfesa Chukwuma Soludo

Gwamna Soludo ya hango shirin magudi

Sai dai, Gwamna Soludo ya yi zargin cewa akwai shirin tafka maguɗi a zaben, inda ya ce wata jam’iyya (ba tare da ya bayyana sunanta ba) tana shirin “musanya sakamakon zaɓe” yayin tattara sakamako.

“Abin da muke ji wanda ke tayar mana da hankali shi ne cewa wata jam’iyya ta riga ta rubuta sakamakon da za ta musanya yayin tattara sakamakon zabe."
“Mun ji cewa sun riga sun gana da INEC domin kada su sanya sakamakon kai tsaye, don su samu damar sauya shi."

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2025: An kama wakilan gwamna da tsabar kudi N1.5bn? An ji gaskiya

- Farfesa Chukwuma Soludo

Soludo ya yi zargin yin magudi a zaben gwamnan Anambra
Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Twitter

Sai dai ya nuna cikakken amincewa da tsarin gudanar zaben, tare da nuna kwarin gwiwar yin nasara.

“Muna da tabbacin cewa tsarin zaben zai yi aikinsa yadda ya kamata. Mutanenmu sun ankara, sun shirya kuma sun haɗa kai."
"Za mu bi tsarin zaben daga rumfar zaɓe zuwa matakin gunduma, daga gunduma zuwa karamar hukuma, sannan zuwa matakin jiha."
“Da zarar tsarin ya yi aiki yadda ya kamata, babu shakka za mu lashe kananan hukumomi 21.”

- Farfesa Chukwuma Soludo

Zaben Anambra: Matasa sun zabi buga kwallo

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu matasa sun zabi fitowa buga kwallon kafa maimakon kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Anambra.

A unguwar Uruotulu da ke cikin birnin Awka, babban birnin jihar, an ga matasa suna buga ƙwallo a gefen titi

Hakazalika Kananan kasuwanni kuma sun buɗe kamar yadda suke yi a kowace rana, yayin da masu sana’ar sayar da abinci suka ci gaba da kasuwanci don tallafawa masu kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Tsakanin APC, APGA: Ƴan Najeriya sun hango wanda zai lashe zaben gwamnan Anambra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng