Zaben Gwamna: Mutanen Anambra Sun Zabi Buga Kwallon Kafa maimakon Kada Kuri'a

Zaben Gwamna: Mutanen Anambra Sun Zabi Buga Kwallon Kafa maimakon Kada Kuri'a

  • A yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra, wasu matasa da mazauna Awka sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum
  • A wasu unguwanni, an ga matasa suna wasan ƙwallon kafa yayin da kananan kasuwanni suka buɗe kamar yadda aka saba a yankuna
  • Sai dai a wasu yankuna kamar Okpuno da Mgbakwu, wasu mutane kaɗan sun fara fitowa yayin da jami’an tsaro suke cigaba da aiki a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra -Yayin da hukumar INEC ke gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra, an lura cewa wasu matasa da mazauna birnin Awka ba su nuna sha’awar fitowa don kada kuri’a ba.

A maimakon haka, an ga wasu a unguwanni suna wasan ƙwallo ko kuma kasuwanci, abin da ke nuna cewa ba kowa ne ya damu da tsarin zaɓen ba.

Kara karanta wannan

TAF Africa ta yi magana kan tsaro yayin da ake zaben gwamnan Anambra

Matasa na kwallo a Anambra
Matasan da suka fita kwallo ana zaben gwamna a Anambra. Hoto: Ebuka Laz
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa a wasu wurare, an fara fitowa a hankali don tantancewa kafin fara kada kuri’a, lamarin da ke nuna cewa wasu har yanzu suna nuna sha’awa a tsarin dimokuraɗiyya.

Matasa sun tafi kwallo maimakon zabe

A yankunan Okpuno da Mgbakwu, da ke kusa da Awka, mutane kaɗan ne ke fitowa don tantance su, yayin da a sauran unguwanni kamar Uruotulu aka ga matasa suna buga ƙwallo a gefen titi.

Kananan kasuwanni kuma sun buɗe kamar yadda suke yi a kowace rana, yayin da masu sana’ar sayar da abinci suka ci gaba da kasuwanci don tallafawa masu kada kuri’a.

Wani mai talla ya ce:

“Ba zan tsaya a gida ba saboda zabe, domin na fi buƙatar neman abin ci. Waɗanda ke son kada kuri’a, su yi hakan.”

Hukumar INEC ta ci gaba da shirye-shirye

A cewar rahotanni daga rumfunan 04 da 005 na Umuobi da Awkuzu, ba a fara zaɓe ba da misalin 8:54 na safe duk da cewa mutane sun riga sun jeru suna jiran jami’an INEC.

Kara karanta wannan

'Ba Fulani ke yi ba': An gano wadanda ke kashe al'umma a Kudancin Najeriya

Sai dai duk da haka, jami’an tsaro sun tabbatar da cewa babu wata matsalar tsaro a wuraren da jama'a suka taru.

Zaben gwamnan Anambra
Masu kada kuri'a sun shiga layin zabe a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Wani ɗan sanda da ya ke tsare wurin ya shaida cewa:

“Komai yana tafiya lafiya, babu wani barazanar tsaro har yanzu.”

Kasuwanci na gudana kusa da masu zaɓe

A kusa da wuraren zaɓe, masu sayar da abinci da kayan masarufi sun ci gaba da kasuwanci domin biyan bukatar masu kada kuri’a.

Wata mai sayar da abinci, Justina Oyibo, ta ce ta fito da safe don yin kasuwa saboda ta san masu zaɓe za su buƙaci abinci.

Hukumar INEC ta bayyana yadda mutane suka fito don kada kuri’a a sassa daban-daban na jihar Anambra a shafinta na X.

Laifuffukan zabe a jihar Anambra

A wani labarin, kun ji cewa a yau ake gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra kuma 'yan takarar AFGA, PDP, APC da ADC da sauransu za su fafata.

Legit Hausa ta yi nazari tare da tattaro laifuffukan da hukumar INEC ta hana mutane yi a lokutan zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi wa shugabannin al'umma 2 yankar rago a jihar Katsina

Daga cikin laifuffukan akwai rajistar zabe fiye da sau daya da kuma tayar da tarzoma a lokacin da ake gudanar da zabe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng