Trump: Sojojin Amurka Sun Dura a Rivers? Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu
- Fadar shugaban kasa ta yi magana bayan yada wani bidiyo a kafofin sadarwa da aka ce sojojin Amurka sun fara sauka a Najeriya
- An yada wani faifan bidiyo da ya bazu a intanet da ke cewa sojojin Amurka sun isa Jihar Rivers domin kaddamar da umarnin Donald Trump
- Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana cewa labarin karya ne don ya hana yada jita-jita
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi karin haske kan bidiyon da ake cewa sojojin Amurka sun sauka a Najeriya
Fadar ya tabbatar da cewa labarin da ake yadawa karya ne saboda babu wani tabbaci da ke nuna sojojin sun iso Najeriya.

Source: Getty Images
An wani bidiyon a ranar 6 ga Nuwamba 2025 da wani mai amfani da X mai suna Spaghetti Mafia (@italian_Spencer) ya wallafa amma yanzu ya gogem ya ce dakarun sun iso jihar Rivers.

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Trump ya yi wa Najeriya
A farkon watan Nuwamba, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki gwamnatin Najeriya bisa zargin kisan kiyashi ga Kiristoci, yana mai cewa zai ɗauki matakin soja idan gwamnati ta kasa kawo ƙarshen matsalar ta’addanci.
Trump ya kuma ce ya umurci rundunar sojoji da ta shirya yaki da ‘yan ta’adda da ake zargi da kisan mutane.
Wannan furuci na Trump ya haifar da matsin lamba daga ƙasashen duniya, ciki har da China, wadda ta bayyana cewa tana goyon bayan ‘yancin kai da ikon Najeriya.

Source: Twitter
Bidiyon zuwan sojojin Amurka da ake yadawa
A cikin rubutunsa wanda ya ce sojojin Amurka sun fara dura a Najeriya, Mafia ya ce tabbas Trump ba da wasa yake ba domin har sojoji sun fara dura a Najeriya.
Mafia ya ce:
“Labari da dumi-dumi: Sojojin Amurka sun sauka a tsibirin Bonny da ke Jihar Rivers!! Donald Trump ba wasa yake ba.”
Wannan rubutu ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a dandalin X inda mutane da dama ke kokarin sanin gaskiar lamarin daga hukumomi.
Abin da fadar shugaban kasa ta ce
Sai dai, mai taimaka wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya gaggauta mayar da martani a shafin X, a ƙarƙashin rubutun ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
A martaninsa, Olusegun ya bayyana cewa:
“Wannan labari ƙarya ne.”
Wannan martanin nasa ya dakatar da yaɗuwar bayanan ƙarya da tayar da hankalin jama’a.
Lamarin ya sake buɗe tattaunawa kan yadda bidiyo da labaran ƙarya ke yawaita a shafukan sada zumunta, musamman lokacin da ake samun labarai marasa tushe.
Fadar shugaban ƙasa ta jaddada muhimmancin tantance gaskiya kafin a yada duk wani abu a intanet.
A ƙarshe, Fadar shugaban ƙasa ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su kasance masu bincike da tantance gaskiya, musamman a wannan zamani da labaran ƙarya ke yawaita a intanet.
Sanata Barau ya soki kalaman Trump
Kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya sake yin magana cikin fushi game da barazanar Donald Trump.
Sanata Barau Jibrin ya caccaki Trump bisa kalamansa kan Najeriya, yana mai cewa sun sabawa dokokin kasa da kasa.
Ya bukaci Trump ya janye kalamansa tare da ba da haƙuri ga ‘yan Najeriya, yana mai jaddada cewa ƙasar ba za ta tsorata ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

