Majalisa Ta Karbi Cin Hancin $10m don Kin Tantance Shugaban NERC? An Ji Gaskiyar Zance
- An yada zargin cewa majalisar dattawa ta karbi cin hanci domin kin tantance Abdullahi Ramat a matsayin shugaban hukumar NERC
- Wani tsohon haidmin tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ne ya jefi shugabannin majalisar dattawa da zargin
- Sai dai, majalisar dattawan ta fito ta yi martani kan zargin mai cewa ta karbi $10m don ganin ba a amince da nadin Ramat ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi martani kan batun dakatar da tantancewa da tabbatar da Abdullahi Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da lantarki ta Najeriya (NERC).
Majalisar ta bayyana zargin cewa shugabanninta sun karɓi cin hanci na Dala miliyan 10 don hana nadin Ramat a matsayin tsabagen karya.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya fitar a ranar Juma'a, 7 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani tsohon mai ba da shawara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, mai suna Alwan Hassan, ne ya yi ikirarin cewa shugabannin majalisar sun karɓi kuɗi don su hana tabbatar da Ramat.
Majalisar dattawa ta kare kanta
A cikin sanarwar da ya fitar, Adaramodu ya karyata wannan zargi, yana mai cewa matakin majalisar ya samo asali ne daga korafe-korafen jama’a da suka biyo bayan nadin na shugaban NERC.
“Shawarar dakatar da tantance Ramat ta samo asali ne daga koke-koke da suka biyo bayan nadin da aka yi masa."
“Ba wannan ne karon farko da majalisar dattawa ta ɗauki irin wannan mataki ba domin mutunta ra’ayoyin jama’a.”
- Yemi Adaramodu
Ya bayyana Alwan Hassan a matsayin mutumin da aka ɗauka aiki don bata sunan majalisa, tare da gargadin cewa majalisar ba za ta bari a bata mata suna da irin waɗannan zarge-zarge na siyasa ba, rahoton ya zo a The Punch.
“Majalisar Dattawa ba za ta ji tsoron ‘yan siyasa ko masu kirkirar labaran karya ba."
"Akwai korafe-korafe masu yawa kan Ramat, kuma ya zama dole mu bi hanyoyi na doka da gaskiya.”
- Yemi Adaramodu

Source: Facebook
Majalisar tarayya za ta kai kara kotu
Adaramodu ya kuma bayyana cewa majalisar za ta kai Alwan Hassan kara kotu, don ya tabbatar da zargin da ya yi a bainar jama’a.
“Ba za mu bari a bata sunan majalisar dattawa da zargi marar hujja ba. Za mu hadu da shi a kotu."
- Yemi Adaramodu
Majalisar dattawa ta jaddada kudirinta na gudanar da ingantaccen tsarin tabbatar da mutanen da aka nada mukamai, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka ba mukami, zai bi tsarin bincike mai gaskiya.
Majalisar dattawa ta bankado satar mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin da majalisar dattawa ta kafa kan satar mai ya fara gabatar da rahoton bincikensa.
Kwamitin ya bayyana cewa ya gano yadda Najeriya ta yi asarar makudan biliyoyi sakamakon satar fetur.
Ya ba gwamnatin tarayya shawara kan matakan da ya kamata ta dauka don magance matsalar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


