Kisan Kiristoci: Shugaba Tinubu Ya Gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
- Bola Tinubu ya karbi bakuncin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, a fadarsa da ke Abuja yau Juma'a
- Fadar shugaban kasa ta ce wannan na cikin tattaunawa da neman shawarwarki da Tinubu ke yi domin tabbatar da hadin kai da yancin addini
- Hakan na zuwa ne biyo bayan barazanar da Amurka ta yi na kawo farmaki Najeriya saboda kisan kiristoci da take zargi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III a ranar Jumma’a a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Rikicin PDP: Shugabananni a jihohi 36 sun raba gardama tsakanin Damagum da tsagin Wike
Rahotanni sun nuna cewa Bola Tinubu da Sarkin Musulmi sun gana tare da tattaunawa kan muhimman barutuwa a ofishin mai girma shugaban kasa da ke Aso Rock Villa.

Source: Twitter
Mai taimakawa shugaban kasa jan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan ganawar Tinubu da Sarkin Musulmi
Ya ce ganawar na cikin jerin tattaunawa da neman shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabannin addini da na gargajiya a Najeriya kan barazanar da Amurka ta yi.
Sanarwar ta ce:
"A ci gaba da tattaunawa da shawarwari da shugabannin addinai da na gargajiya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’adu Abubakar III, yau a Fadar Shugaban Ƙasa.
"Wannan ganawa ta zo ne ‘yan kwanaki kaɗan bayan ya gana da babban limamin Katolika na Abuja, Bishof Ignatius Ayau Kaigama, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma da tabbatar da ɗorewar ‘yancin addini a ƙasar nan"
Barazanar da Trump ya yi wa Najeriya
Hakan dai na zuwa ne bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke da babar matsala kan yancin addini.
Shugaba Trump ya kuma yi barazanar cewa matukar gwamnatin Najeriya ba ta gaggauta daukar matakin kare kiristoci ba, Amurka za ta kawo farmaki.
Donald Trump ya kuma umarci ma'aikatar yaki ta Amurka ta fara shirye-shiryen yiwuwar kawo faramki Najeriya domin murkushe yan ta'adda.
Wane mataki Shugaba Tinubu ya dauka?
Tuni dai Shugaba Tinubu ya maida martani ga Trump, yana mai cewa Najeriya kasa daya ce da ke bin tafarkin dimokuradiyya wanda ya ba kowa yancin addini.
Tinubu ya ce zargin ana yi wa kiristoci kasan kare dangi ya saba wa hakikanin abin da ke faruwa a Najeriya, inda ya ce babu wariya ko cin zarafin addini a kasar.
Sai dai duk da haka Bola Tinubu ya fara ganawa da shugabannin addinai domin neman shawarwari kan wannan barazana ta Trump.

Source: Twitter
Sakamakon haka ne, Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi yau Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2025, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
'Wane hali muke ciki,' Tsohon hadiminsa ya nemi Tinubu ya yi bayani kan barazanar Trump
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya raka Sarkin Musulmi zuwa wannan ganawa da aka bayyana a matsayin “mai muhimmanci”.
Tinubu ya kwantar da hankulan yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankulansu kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
Shugaban kasan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa tana aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan.
Ministan yada labara, Muhammed Idris, ya ce gwamnatin Bola Tinubu na bin dukkannin matakan da suka dace don tabbatar da cewa Najeriya ta samu ingantaccen tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
