'Farashin Abinci Ya Kara Yin Kasa Warwas a Najeriya,' Minista Ya Bayyana Dalili

'Farashin Abinci Ya Kara Yin Kasa Warwas a Najeriya,' Minista Ya Bayyana Dalili

  • Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari, ya ce Najeriya na samun ci gaba wajen cimma ikon samar da abinci da tsaron abinci
  • Sakamakon wasu shirye-shirye da gwamnati ta kawo, kamar NAGS–Agro-Pocket, NPSTP, an samu saukar farashin abinci
  • Sabon shirin na NPSTP zai kuma magance asarar kayan amfanin gona bayan girbi, wanda ke kai darajar dala biliyan 10

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna – Ministan noma da rsaron abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa farashin kayan abinci yasauka kasa sosai sakamakon matakan da gwamnati ta dauka.

Sanata Kyari ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar noma ta kasa karo na 47 da aka gudanar a dakin taro na Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, daga 3 zuwa 7 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

Abinci
Hoton wani dan kasuwa a cikin shagonsa da kuma kashi kashi na kayan abinci. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Minista ya magantu kan tsaron abinci

Taron ya hada da kwamishinonin noma na jihohi, masu ruwa da tsaki, ‘yan kasuwa, da wakilai daga majalisar dokoki domin tattauna ci gaban noma a kasar, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kyari ya ce noma shi ne ginshikin tattalin arzikin Najeriya, wanda yake samar da aikin yi ga mafi yawan al’umma tare da bayar da gudunmuwar fiye da kashi 25% ga GDP.

A cewar ministan:

“Noma ne tushen gina sabuwar rayuwa ga 'yan kasarmu. Wannan gwamnati ta sanya tsaron abinci a matsayin ginshiki na wanzar zaman lafiyar al'umma.
“Tsaron abinci yana nufin kowane gida ya samu wadataccen abinci, kuma a saye shi da araha. Wannan shi ne matakin tabbatar da ingantaccen tsarin noma da kowa zai amfana da shi."

Shirin Agro-Pocket da fadada noman alkama

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta karfafa shirin noma na NAGS–Agro-Pocket tare da goyon bayan bankin AfDB da gwamnatocin jihohi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako mutum 500 da suka sace bayan Uba Sani ya dauki mataki

Shirin yana ba manoma tallafin taki, iri, da kayan noman zamani a kan lokaci domin bunkasa amfanin gona, in ji rahoton This Day.

Sanata Kyari ya ce:

"Mun kara yawan manoman da ke amfana da shirin, kuma hakan yana taimaka wa wajen tabbatar da wadatuwar abinci a kasar nan.”

Ya bayyana cewa an fadada noman alkama a Najeriya, inda yanzu suka zarce jihohi 15 da aka samu a shekarar noman 2023/2024.

Haka kuma, gwamnatin ta kaddamar da noman alkamar damina a jihohin Plateau, Taraba, da Cross River — wani cigaba da aka samu daga cibiyar bincike ta Tafkin Chadi.

Ministan noma, Abubakar Kyari
Hoton ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari. Hoto: @SenatorAKyari
Source: Twitter

Sabon shirin rage asarar kayan amfanin gona

Ministan noman ya kuma sanar da kaddamar da sabon shirin NPSTP da aka kirkira tare da shirin AGRA, wanda zai rage asarar amfanin gona na dala biliyan 10 da manoma ke yi bayan girbi.

Sanata Kyari ya ce wannan shiri zai magance matsalolin ajiya, sufuri, da sarrafa kayan amfanin gona domin kara darajar su kafin kai su kasuwa.

Ministan ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa manoma ta hanyar amfani da bayanan fasaha, horo, da hadin gwiwa da kamfanonin masu zaman kansu.

Kara karanta wannan

'Ba na jin tsoron Trump,' An samu sabani tsakanin Barau da Akpabio a majalisa

Farashin abinci ya sauka a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce an samu saukar hauhawar farashin kaya a Najeriya zuwa 18.02%.

Saukar farashin kayayyakin zuwa 18.02% shi ne mafi ƙanƙanta da aka samu a Najeriya cikin shekaru uku, cewar rahoton hukumar NBS.

Rahoton ya nuna cewa jihohi, Ekiti, Rivers, da Nasarawa ne suka fi tsadar farashin abinci, yayin da Bauchi, Niger, da Anambra suka fi sauƙin kayan abinci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com