Zargin Ta'addanci: Kotun Tarayya Ta Saka Ranar Yanke Hukunci a kan Shari'ar Nnamdi Kanu

Zargin Ta'addanci: Kotun Tarayya Ta Saka Ranar Yanke Hukunci a kan Shari'ar Nnamdi Kanu

  • Babban kotun tarayya da ke sauraron shari'ar shugaban kungiyar 'yan ta'addan Nnamdi Kanu ta shirya yanke hukunci
  • Gwamnatin Najeriya na shari'a da Nnamdi Kanu a kan zargin ta'addanci wanda ya zafafa fafutukar ballewa daga kasar nan
  • A zaman da aka yi na ranar Juma'a, Kanu ya bai wa kotu wasu dalilai da su ka hana shi mika takardu, kuma ta ba shi dama kafin gama zaman

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayyana cewa an shirya yanke hunkunci a kan zargin ta'addanci da kasar nan ke yi wa Nnamdi Kanu.

Kotu ta sanar da haka ne a zamanta da ya gudana a ranar Juma'a, 7 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya ta fadi matsayarta a kan zargin ta'addanci da Najeriya ke yi wa Kanu.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Trump, gwamnatin Najeriya ta yi magana kan shari'ar 'yan ta'adda

Nnamdi Kanu zai san makomarsa
Hoton Nnamdi Kanu a kotun tarayya Hoto: @MArinze2993
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa alkalin, James Omotosho, ya tsayar da ranar ne bayan Kanu ya gaza fara gabatar da shaidunsa kamar yadda aka ba shi dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake gudanar da shari'ar Nnamdi Kanu

Punch ta wallafa cewa Shugaban kungiyar 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu ya dakatar da lauyoyinsa, yana son ya kare kansa, yana cewa babu dalilin tuhumarsa da ta'addanci.

A ci gaba da shari'ar a ranar Juma'a, alkalin ya umarci a kai rijistar kotun zuwa cikin zauren don Kanu ya samu ya mika wasu takardu da yake so ya gabatar.

Har ila yau, ya nemi a soke dukkannin shaidun da aka yi a shari’ar tun farko saboda ya ce an gina shari’ar ne bisa rashin gaskiya.

Ya dage a kan cewa dokar tarayya, ta sashe 36(12) na kundin tsarin mulkin 1999, ba ta fayyace ta’addanci a matsayin laifi ba a Najeriya, inda ya ce babu doka a rubuce da ta tantance ta'addanci.

Kara karanta wannan

Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga

Nnamdi Kanu ya kara da zargin hukumar tsaron farin kayan Najeriya, DSS da ci gaba da karya doka wajen keta masa hakkinsa na 'dan adam.

An ba Nnamdi Kanu damar kare kansa

A zaman kotun, shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar da cewa yana da muhimmin takarda da yake son ya mika amma bai samu damar yin hakan ba.

Bayan wannan koke, alkalin kotu, James Omotosho, ya bayar da umarnin cewa a ɗan mayar da rijistar kotu cikin zauren shari’a domin a ba Kanu damar cikawa da mika takardun nasa yadda doka ta tanada.

Za a yanke wa Kanu hukunci a watan Nuwamba
Hoton shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: Hoto: @MArinze2993
Source: Twitter

Sakamakon haka, kotun ta dakatar da ci gaba da shari’ar na tsawon awa ɗaya don ba shi lokaci ya kammala aikin nasa.

Kanu yana roƙon kotu ta goge rokon da ya yi na kin amsa laifi da aka rubuta a kundin shari’ar saboda, a cewarsa, an gurfanar da shi ne cikin karya da saba wa sashi 36 na kundin tsarin mulki.

Ya yi zargin cewa tsarin da aka bi wajen gurfanar da shi bai bi ƙa’idojin adalci ba, kuma hakan ne ya sa yake neman a soke shi gaba daya.

Kara karanta wannan

'Sai an biya kudi ake ganin Tinubu a Aso Villa,' Sanata Ndume ya yi sabuwar bankada

An dage shari'ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025 domin a yanke hukunci.

Atiku na son a fito da Nnamdi Kanu

A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga neman sakin jagoran ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

A cewar Atiku, idan gwamnati ta ƙi sakin Kanu, to wajibi ne ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa ka’ida domin a kawo karshen tsare shi da aka yi na tsawon shekaru a kan zargin ta'addanci.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023 karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng