Gwamnati za Ta Kawo Tsarin da Jiragen Kasa za Su Yi Aiki a Kowace Jihar Najeriya

Gwamnati za Ta Kawo Tsarin da Jiragen Kasa za Su Yi Aiki a Kowace Jihar Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin kaddamar da sabuwar taswira domin hada jihohi 36 da Abuja da titin layin dogo
  • Shugaban hukumar jiragen kasa, Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan a taron sufuri na kasa karo na bakwai da aka yi
  • Ya ce shirin na da alaka da manufar 'Renewed Hope' ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta bunkasa tattalin arziki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Abuja – Hukumar NRC ta sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta kaddamar da sabuwar taswirar layin dogo a Najeriya.

Taswirar za ta tabbatar da cewa dukkan jihohi 36 na kasar da babban birnin tarayya Abuja sun samu layin dogo kai tsaye.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya da wani jirgin kasa. Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Railway Corporation
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa shugaban NRC, Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron sufuri na kasa karo na bakwai da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin kasa zai ratsa jihohi 36 da Abuja

Opeifa ya bayyana cewa sabuwar taswirar za ta bai wa kowace jiha damar shiga cikin tsarin layin dogon kasa ba tare da biyan kudin aikin samar da jiragen kasa ba.

Za a yi haka ne sakamakon sauyin doka da ya sanya harkar layin dogo cikin jerin ayyukan da jihohi da tarayya ke da ikon aiwatarwa tare.

A cewarsa:

“An tsara wannan taswira ne domin bai wa dukkan jihohi damar amfani da layukan dogo kyauta.”

Ya kara da cewa manufar ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin jihohi da na tarayya domin tabbatar da cewa ana amfana da layin dogo a kasa yadda ya kamata.

Jihohin da za su amfana a karon farko

The Cable ta rahoto cewa Opeifa ya bayyana cewa yanzu haka akwai layin dogo daga Legas zuwa Kano kuma jihohin da suke kan hanyar za su amfana.

Kara karanta wannan

TUC: Yan kwadago sun taso Gwamnatin Tinubu kan shirin kakaba harajin 15% kan fetur

“Idan jiharka tana cikin wannan hanya, za ka iya gudanar da ayyukan sufuri a kai. Legas da Filato sun riga sun fara, kuma mun bude kofa ga sauran jihohi,”

- Inji shi

Ya ce jihohin Ogun da Oyo suna da layukan dogo da za a iya amfani da su, yayin da Edo, Delta, Kogi, Kaduna, Kano da Neja suma za su iya shiga cikin tsarin.

Cigaba da fadada jigila da jirgin kasa

Shugaban NRC ya bayyana cewa ana ci gaba da fadada jigilar kaya da jirgin kasa, ciki har da kayayyaki irin su gypsum, siminti da kayan aikin gina bututun iskar gas na AKK.

Ya ce wannan bangare na aikin yana kara rage cunkoson tituna tare da samar da hanyoyin kasuwanci mai dorewa tsakanin jihohi da tashoshin ruwa.

Jirgin kasan Najeriya
Hoton wani jirgin kasa na daukar mutane. Hoto: Nigerian Railway Corporation
Source: Twitter

Opeifa ya bayyana cewa hukumar NRC ta samar da tsari na dogon lokaci da ke nufin inganta layin dogo a Najeriya.

Majalisa na binciken kwangilolin jiragen kasa

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta kafa kwamiti na musamman domin binciken wasu jiragen kasa da aka samar a lokacin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Trump: Najeriya ta gana da jakadun kasashe, an yi maganar Shari'ar Musulunci

Shugaban majalisar dattawa ya ce dole a yi bincike domin gwamnati ta kashe makudan kudi wajen samar da jiragen kuma suna lalacewa da wuri.

Yayin da aka kafa kwamitin bincike, majalisar ta ce za a hukunta duk wanda aka samu da laifi wajen rashin aiki maras inganci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng