An Gargadi Amurka bayan Barazana kan Shari’ar Musulunci, Gwamnonin Arewa 12

An Gargadi Amurka bayan Barazana kan Shari’ar Musulunci, Gwamnonin Arewa 12

  • Kungiyar MURIC ta soki Amurka kan kira da ta yi na a soke Shari’a da barazanar kakabawa gwamnonin Arewa 12 takunkumi
  • MURIC ta bayyana hakan da neman dakile dimukradiyya da kuma kiran hakan a matsayinta “rashin adalci da ladabi”
  • Farfesa Ishaq Akintola ya ce matakin Amurka na nuna tsoma baki cikin harkokin ƙasa mai cin gashin kanta, kuma yana barazana ga zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta yi kaca-kaca da gwamnatin Amurka bisa kira da ta yi na soke tsarin Shari’a.

Haka kuma kungiyar MURIC ta bayyana damuwa kan barazanar kakabawa gwamnonin Arewa 12 takunkumi da Amurka ta yi.

MURIC ta soki Amurka kan shiga lamarin Najeriya
Shugaban MURIC, Donald Trump da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

MURIC ta zargi Amurka da shirin dakile shari'a

Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan gudanarwa na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, a jiya Alhamis 6 ga watan Nuwambar 2025, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

'Da gaske ne ana kisan kiyashi a Najeriya,' Jigon APC ya goyi bayan Donald Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akintola ya ce kalaman da suka fito daga Amurka “babu adalci ko kadan, sun saba dimokuraɗiyya kuma suna iya tayar da rikici.”

Ya zargi wasu ‘yan majalisar Amurka da ƙoƙarin tilasta tsarin rayuwar Amurkawa ga Musulmai a duniya, ciki har da na Najeriya.

Akintola ya bayyana cewa an kafa Shari’a ne bisa ka’idar dimokuraɗiyya da amincewar mafi rinjayen jama’a a jihohin da ake amfani da ita.

Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Yadda aka samar da shari'ar Musulunci a Arewa

Farfesan ya jaddada cewa majalisun dokoki na jihohin da ke amfani da Shari’a ne suka amince da ita bayan bin dukkan matakan da doka ta tanada.

Don haka, duk wani yunƙuri daga ƙasar waje na soke ta yana nufin tsoma baki cikin harkokin cikin gida da kuma take dokokin kasa da kasa.

Ya ce:

“Wannan matakin zai lalata ka’idar dimokuraɗiyya, ya tauye ‘yancin magana da ‘yancin addini.”

Haka kuma, MURIC ta yi tir da barazanar da aka yi wa gwamnonin Arewa 12, tana cewa an zaɓe su a sahihin tsarin zabe mai gaskiya da amincewar kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Janye biza: Wole Soyinka ya dura kan Trump, ya kira shi mai mulkin kama karya

Kungiyar ta nemi ‘yan majalisar Amurka su bar dimokuraɗiyyar Najeriya ta ci gaba, tana mai jaddada cewa Shari’a zabin Musulman Najeriya ne, kuma duk wani ƙoƙari na takura musu ko tsoratar da gwamnoni a Arewa ba zai karbu ba.

Ya ce:

“Su ne halattattun shugabannin jihohinsu. Barazanar Amurka ga waɗannan gwamnonin abin ƙi ne da kuma take tsarin zaɓen Najeriya da mutuncin al’adun Arewacin ƙasar.”

MURIC ta zargi gwamnatin Tinubu da fifita Kiristoci

A baya, mun kawo muku cewa kungiyar kare haƙƙin Musulmi, MURIC, ta zargi gwamnatin tarayya da nuna bambanci a harkar jigilar fasinjoji kyauta yayin bukukuwan addini.

MURIC ta ce gwamnatin ta ware Kiristoci da ba su damar hawa jirgin kasa kyauta a lokacin Kirsimeti, amma ba ta yi hakan ga Musulmi a lokacin sallah ba.

Ta yi kira da a duba tsarin hutun karshen mako da bukukuwan kasa da ta ce sun fi karkata ga Kiristanci tun daga zamanin mulkin mallaka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.