A Karon Farko, Tinubu Ya Fadi Abin da Najeriya ke Yi kan Barazanar Trump

A Karon Farko, Tinubu Ya Fadi Abin da Najeriya ke Yi kan Barazanar Trump

  • A karon farko tun bayan da Shugaban Amurka, Donald J. Trump ya zargi Najeriya da zuba ido ana kashe kiristoci, Bola Tinubu ya yi magana
  • A jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa tana kokarin magance zargin Amurka ta hanyar diflomasiyya
  • Ya bayyana haka bayan Trump ya ce kasarsa za ta aiko dakuru zuwa Najeriya, kuma tuni aka fitar da tsarin yadda za ta kawo harin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da martani ga barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Najeriya.

Trump dai ya yi kalamai masu tsauri a kan kasar nan, har ya bayyana yiwuwar kawo wa Najeriya hari da dakatar da tallafi saboda zargin kashe Kiristoci a ƙasar.

Kara karanta wannan

Trump ya kara nuna yatsa ga Najeriya, ya ce ba za a ji da dadi ba

Shugaban kasa Tinubu ya yi martani ga Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya Hoto: Donald J Trump/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Trump ya bayyana cewa Najeriya da zama kasar da ake da damuwa a kanta, saboda zargin gwamnati da kin daukar mataki kan kisan 'yan uwansa' kiristoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amsar Tinubu ga Trump kan kisan kiristoci

The Sun Nigeria ta wallafa cewa Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta karyata zargin cewa akwai kisan kiristoci a kasar nan saboda addininsu.

Shugaban kasan ya tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yancin addini da doka ta tabbatar da hakan.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce:

“Mafi muhimmanci shi ne, duk da matsin lamba na siyasa da tsoron al’umma, za mu ci gaba da tattaunawa da abokan hulɗa na duniya ta hanyar diflomasiyya.”

Ya ƙara da cewa gwamnati tana da niyyar ci gaba da yaƙi da ta’addanci tare da tabbatar da haɗin kan ƙasa bisa tsarin gwamnatinsa.

Gwamnati ba ta razana ba - Tinubu

A karin bayaninsa, Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa an buɗe hanyoyin sadarwa da ƙasashen duniya ciki har da Amurka don tattauna matsalar.

Kara karanta wannan

Trump: Cacar baki ta balle tsakanin China da Amurka a kan Najeriya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce za a murkushe ta'addanci
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya ce:

“Gwamnatin Najeriya ba ta cikin halin firgici. Muna mayar da martani a cikin natsuwa, domin kare mutuncin ƙasarmu da tabbatar da tsaron ’yan ƙasa.”

Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ƙasa ce mai haƙuri da juna ta fuskar addini, kuma gwamnati ba za ta bari matsalar ta’addanci ta raba ƙasa ba.

Ya jaddada cewa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya, musamman Amurka, na da muhimmanci wajen kawo ƙarshen ta’addanci.

Kiran Isra'ila ga Najeriya bayan kalaman Trump

A baya, mun wallafa cewa jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zauna lafiya da juna cikin fahimtar juna da girmama kowa.

Freeman ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin wani taron tattaunawa tsakanin shugabannin Musulmi, Kiristoci da Yahudawa da aka gudanar a Abuja.

Jakadan ya bayyana cewa wannan tattaunawa ta zo a lokaci mai muhimmanci, yayin da duniya ke fuskantar ƙalubale masu nasaba da rashin fahimta da rarrabuwar kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng