An Fara: Ƙungiyar ISWAP Ta Yi Zazzafan Martani ga Trump, Ta Shawarci Mayaƙanta
- Kungiyar ISWAP ta mayar da martani ga kalaman Donald Trump bayan ya yi barazanar kawo hari a Najeriya game da rashin tsaro
- Yayin martanin, ISWAP ta kira shugaban Amurka “makaryaci kuma dan kama-karya” da ke neman ya jawo rikici a Najeriya
- Kungiyar ta zargi Trump da yin aiki karkashin tasirin Kirista da Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi domin kawo rigima a kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta fitar da sanarwa tana mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka, Donald Trump.
Martanin kungiyar ISWAP na zuwa ne bayan Trump ya ce zai kai farmaki a Najeriya kan zargin kisan Kiristoci da 'yan ta'adda ke yi.

Source: Getty Images
A cikin saƙon da ta yada ta hanyar kafafenta na sada zumunta wanda Zagazola Makama ta samu, ISWAP ta kira Trump dan kama-karya kuma marar tunani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Trump ya yi wa Najeriya
Martanin ISWAP din na zuwa ne bayan Donald Trump ya gargadi Najeriya da ta murkushe yan ta'adda da ke kisan Kiristoci.
Trump ya ce idan har gwamnatin Najeriya ta gagara kawo karshen kisan gilla da ake yi wa Kiristoci to zai dauki matakin soji kan kasar.
Wannan barazana ya jawo maganganu da mabambantan ra'ayoyi a Najeriya da fadin duniya baki daya.

Source: Original
Martanin ISWAP ga Trump game da barazanarsa
Kungiyar ta ce tana zarginsa da yin biyayya ga wasu Kirista da Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi da suka rinjayi gwamnatinsa a baya.
ISWAP ta bayyana kalaman Trump a matsayin yunkuri na Amurka don nuna kanta a matsayin mai kare Kiristoci na duniya.
Ta ce wannan salon zai jawo ta cikin sababbin rikice-rikice a kasashen Kongo da Mozambik, inda ake fama da hare-haren ‘yan tada kayar baya.
Umarnin da ISWAP ta ba mayakanta
ISWAP ta kara da cewa wannan na cikin dabarar fadada yaki da ISIS da kuma sauran yankuna da dama; kamar Iraki, Siriya, Somaliya, Afghanistan da Tafkin Chadi, domin ta biyan bukaar kanta.
Kungiyar ta kuma umarci mayakanta su guji manyan taruka, su rage amfani da wayoyi, da kuma gujewa zirga-zirga marasa muhimmanci, tana cewa akwai yiwuwar karuwar leƙen asiri da hare-haren jiragen yaki na Amurka.
A ƙarshe, ISWAP ta kira Musulmai a yammacin Afirka da su haɗa kai, tana zargin kasashen yamma da aikata “laifuka kan Musulman Afirka” da kuma amfani da kalmar kare Kiristoci a matsayin hujjar kai farmaki.
An gwabza fada tsakanin ISWAP da Boko Haram
A baya, kun ji cewa mayakan Boko Haram sun kai hari kan sansanonin ISWAP a Abadam, Jihar Borno, inda suka yi musu mummunan kisan gilla.
ISWAP ta karɓi sababbin makamai ta jiragen ruwa biyu daga tafkin Chadi domin shirin ramuwar gayya kan Boko Haram bayan hallaka wasu daga mayakansu a fafatawar da aka yi.
Rikicin na kara tsananta, inda aka samu asarar manyan kwamandojin ISWAP da kuma shirin sake kai farmaki a tsakaninsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

