'Yan Bindiga Sun Sako Mutum 500 da Suka Sace bayan Uba Sani Ya Dauki Mataki

'Yan Bindiga Sun Sako Mutum 500 da Suka Sace bayan Uba Sani Ya Dauki Mataki

  • Gwamnatin Kaduna ta ce ta kubutar da mutane sama da 500 ta hanyar tsarin tattaunawa da 'yan ta'adda a jihar
  • Tsarin “zaman lafiya a Kaduna” yana mayar da hankali kan samar da ilimi, inganta lafiya da tallafawa rayuwar al’umma
  • Gwamna Uba Sani na ci gaba da amfani da tattaunawa wajen kawo karshen ta’addanci a jihar maimakon amfani da karfi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin Gwamna Uba Sani, ta bayyana cewa ta samu nasarar kubutar da fiye da mutane 500 da aka sace.

Gwamnatin ta ce ta yi amfani da sabon tsarin samar da zaman lafiya wanda bai shafi biyan kudin fansa ko amfani da karfin makami kan 'yan bindiga ba.

Gwamnatin Uba Sani ta yi amfani da sabon tsarin tsaro da ya jawo kubutar mutane 500 daga 'yan bindiga
Gwamna Uba Sani ya na jawabi a lokacin bude kasuwar Birnin Gwari da aka rufe saboda matsalar tsaro. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Tsarin samar da tsaro na jihar Kaduna

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan yayin taron “aikin jarida a bangaren zaman lafiya” da aka gudanar a Kaduna a ranar Laraba, in ji Premium Times.

Kara karanta wannan

Dalilin Peter Obi na zagaya Najeriya, ya na ba makarantu kyautar miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed Maiyaki ya ce wannan tsarin da aka kirkiro ya samu goyon bayan ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro (ONSA) da kwamitin zaman lafiya na Kaduna.

Kwamishinan ya bayyana cewa tsarin ya mayar da hankali ne kan ilimi, kiwon lafiya, da tallafin tattalin arziki ga al’ummomin da rikice-rikice suka shafa.

“Ba za ka iya jefa bam domin ka samu zaman lafiya ba. Sai an samar da aminci tsakanin jama'a ne za a iya gina zaman lafiya."

- Ahmed Maiyaki.

“Ba mu biya su ko sisi ba" — Maiyaki

Maiyaki ya bayyana cewa bayan shekaru da dama na hare-hare da sace-sacen mutane, gwamnatin Kaduna ta fahimci cewa zaman lafiya na gaskiya ba zai samu da makami kawai ba, sai da magance abubuwan da suka jawo matsalar tsaron.

Ya ce canjin tunani ya fara ne lokacin da wasu shugabannin ‘yan bindiga suka roƙi gwamnati ta buɗe kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya da aka rufe saboda hare-hare.

Kara karanta wannan

Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga

“Mun amince, domin waɗannan bukatu na rayuwa ne, ba don fansa ba. Ba mu ba su ko sisi ba — biyan bukatunsu da aka yi ya dawo martabar rayuwar al’umma."

- Ahmed Maiyaki.

Kwamishinan ya kara da cewa tsakanin 2015 zuwa 2023, Kaduna ta fuskanci matsalolin tsaro fiye da 1,160 da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 4,876, in ji rahoton The Nation.

Ya ce an yi garkuwa da dubban mutane yayin da a 2021 kadai, mutane 1,192 suka mutu, sama da 3,000 aka yi garkuwa da su, lamarin da ya janyo rufe makarantu 142 da cibiyoyin lafiya 192 a fadin jihar

An samar da zaman lafiya a garuruwan da suka fuskanci matsalar tsaro a Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zaman lafiya: An bude kasuwanni da gonaki

Maiyaki ya ce sabon tsarin samar da tsaro ya mayar da hankali kan tattara bayanan leƙen asiri, tattaunawa, da kuma haɗa kan jama’a don samar da ci gaba.

A cewarsa, tsarin ya taimaka wajen farfado da fiye da hekta 500,000 na gonaki, buɗe kasuwannin karkara, da dawo da hanyoyin sufuri da a da suka kasance masu hatsari.

Gwamna Uba Sani dai ya sha nanata cewa gwamnatin sa za ta yi amfani da hanyoyin tattaunawa da 'yan ta'adda, maimakon amfani da karfin makami.

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanin sojoji a cikinsu

'Yan bindiga sun dawo shiga jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kaduna ta kulla yarjejeniya da ‘yan bindiga, wacce ta ba su damar shiga kasuwanni da asibitoci.

Yarjejeniyar ta kawo sauyi a yankin Birnin Gwari, inda jama’a ke jin sassauci bayan shekaru na fargaba da satar mutane da 'yan bindiga ke yi.

Shugabannin al’umma sun ce zaman lafiya ya dawo, sai dai suna kira da a ci gaba da kiyaye yarjejeniyar domin dorewar alkawarin da aka dauka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com